Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Babban Hafsan Tsaro na ƙasa, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa yunwa da talauci ba kawai matsalolin zamantakewa ba ne a yanzu, sun koma barazana ga tsaron ƙasa baki ɗaya.
Janar Musa ya bayyana hakan ne a lokacin buɗe taron bitar tsaro na ƙasa karo na 14 da ƙungiyar Tsoffin ɗaliban Kwalejin Tsaro ta ƙasa (AANDEC) ta shirya a ranar Litinin a birnin Abuja.
Taken taron shi ne: “Yadda Za a Yaƙi Yunwa da Talauci Domin Samar da Zaman Lafiya da Cigaba mai ɗorewa a Nijeriya”, wanda aka shirya tare da haɗin gwiwar Ofishin Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro da Kwalejin Tsaro ta ƙasa (NDC).
Babban Hafsan, wanda Kwamandan Horar da Sojoji na ƙasa, Rear Admiral Ibrahim Shetimma ya wakilta, ya jaddada cewa akwai buƙatar haɗin gwiwar ƙasa baki ɗaya don yaƙi da yunwa da talauci, yana mai bayyana yadda hakan ke shafar tsaron cikin gida.
Ya yaba wa masu shirya taron bisa ƙirƙirar wani muhimmin dandali na tattauna matsalolin tsaro da cigaban Nijeriya.
