Da Ɗumi-Ɗumi: Ganduje ya yi murabus daga shugabancin APC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Rahotanni daga gidajen jaridu sun bayyana cewa, Shugaban Jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje ya sanar da yin murabus daga muƙaminsa, lamarin da tuni ya fara aiki nan take.

Ganduje, wanda tsohon gwamnan Jihar Kano ne, ya ce ya ɗauki matakin ne saboda dalilai masu alaƙa da kiwon lafiyarsa, yana mai bayyana hakan a matsayin abinda shi ne daidai a gare shi.

Hakan na zuwa ne a lokacin da ake yaɗa jita-jitar cewa jam’iyyar na shirin gudanar da sauye-sauye.

Kawo yanzu babu wani mai muƙami daga cikin APC da ya yi tsokaci game da wanda zai gaje shi ko kuma wani shiri da ta ke yi, kamar yadda ‘paradigmnews’ ta ruwaito daga ‘premiumtimes’.

By Babaji