Gidauniyar British American Tobacco ta ƙaddamar da rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana a Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gidauniyar British American Tobacco Nigeriya (BATN) ta ƙaddamar da rijiyar burtsatse da famfon hannu masu amfani da hasken rana, mai samar da lita 20,000 na ruwa kullum a rana ga al’ummar Ƴankifi da ke ƙaramar hukumar Ghari a jihar Kano.

An kaddamar da wannan aikin ne a ranar Talata da ta gabata. Shugaban gidauniyar, Oludare Odusanya, ya bayyana cewa manufar wannan aikin shi ne inganta rayuwar ‘yan Najeriya, musamman mazauna karkara, ta hanyar samar da ruwa mai tsafta.

“A binciken da muka gudanar al’ummar Ƴankifi na fama da matsanancin rashin ruwa, inda suke tafiya mai nisa domin samo ruwa. Babu wata al’umma da za ta ci gaba da wannan hali. Wannan ne ya sa muka yanke shawarar aiwatar da wannan aiki a gare su,” in ji Odusanya.

Ya ƙara da cewa “Mun fara aikin kusan wata guda da ya wuce, kuma yanzu an kammala shi tare da miƙa shi ga al’umma domin amfana da ruwan sha mai tsafta,”

“Wannan famfo zai riƙa fitar da lita 20,000 na ruwa a kullum daga rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana. Dukkan waɗannan na’urori mun mika su ga al’umma. Ba mu da hannu a kula da su daga yanzu, ku ne za ku tabbatar da kula da su don amfanin kowa da kowa,” in ji Odusanya.

A nasa jawabin, kwamishinan albarkatun ruwa na Jihar Kano, Alhaji Umar Haruna Doguwa, ya ce tun lokacin da Gidauniyar Brish American Tobacco Nigeriya ta zo Kano, sun sanar da mu kuma sun sanar da gwamnan Jihar Kano kuma aka ba su zaɓin wurare biyu, Warawa da Ƴankifi. Bayan tantancewa, aka ga Ƴankifi ce ke cikin matsanancin buƙatar ruwa.

“Daga yau wannan aiki ba na Gidauniyar BATN bane, naku ne. Idan kun kula da shi, zai amfani kowa; idan kuma ba ku kula ba, ku ne za ku fuskanci matsalolin da za su biyo baya. Na san ba za ku bari ya lalace ba, saboda kun san wahalar da kuka sha kafin wannan aikin. Yana da matuƙar muhimmanci ku kafa wani tsarin kariya ga wannan muhimmiyar cibiyar,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa: “Mun tattauna da shugaban ƙaramar hukuma, kuma mun roƙe shi za’a samar da mutane biyu daga cikin wannan gari nan za a ɗauke su aiki domin su rika sa ido da kula da wannan cibiyar.”

“Ba daidai bane ‘ya’yanmu da ya kamata a ce suna zuwa makaranta amma sai su buge da ɗibar ruwa muna so kowane yaro ya sami ilimi kamar yadda muka samu, wata rana su ma za su iya zama gwamna ko kwamishina,” in ji kwamishinan albarkatun ruwa.

Ishaka Adamu daga Ƴankifi ya bayyana cewa kusan shekaru 30 al’ummarsu ke fama da matsalar rashin ruwa, kuma yace bai taɓa ganin irin wannan cigaba ba da garin ya samu ba.

Ya ce: “Na taso a gidanmu a jaki ake zuwa dam domin ɗebo ruwa. Hakan ya zama wani ɓangare na rayuwarmu. Daga baya muka fara amfani da keke. Idan a yau ba ka da keke ko babur don ɗebo ruwa, to kana cikin matsala, amma yanzu, Alhamdulillah, ba mu da abin cewa sai godiya ga gudauniyar British America Tobacco Nigeriya,” in ji Ishaka Adamu.

Taron ƙaddamarwar ya samu halartar alummomi daban-daban, ciki har da wakilan na’aikatar albarkatun ruwa ta Jihar Kano, wakilin shugaban ƙaramar hukuma, Magajin Garin Kano, kansilan ruwa da kuma al’ummomin garin maza da mata.

By ukarofi