Rikicin da ya dabaibaye Gaza ya ɗauki sabon salo na tashin hankali, inda rahotanni daga ma’aikatar lafiya ta Falasɗinu suka tabbatar da cewa dakarun Isra’ila sun hallaka Falasdinawa 44 a safiyar Talata, a lokacin da suke jiran kayan agaji da ke kan hanyarsu zuwa kudancin Gaza.
Shaidu da ma’aikatan lafiya sun bayyana cewa dakarun Isra’ila da jiragen leƙen asiri sun buɗe wuta a kan ɗaruruwan jama’a da suka taru a kan hanyar Salah al-Din kusa da Wadi Gaza, inda motocin ɗaukar agaji ke ƙoƙarin shigowa. Wannan hari ya jikkata wasu 146, ciki har da 62 da ke cikin mawuyacin hali.
“Kisan kiyashi ne!” cewar wani shaidan gani da ido, Ahmed Halawa. “Harbinmu aka riƙa yi duk da muna gudu. Mutane da dama sun faɗi matattu ko suna zubar da jini.”
Rahotanni sun ruwaito cewa mutanen da suka taru sun fito ne daga sassa daban-daban na Gaza domin samun abinci da kayan tallafi da ke shigowa, amma sai suka fuskanci ruwan wuta daga tankokin yaƙi da jiragen drone na Isra’ila.
“Na ga mutane uku a ƙasa, sun daina motsi. Wasu da dama kuwa suna ihu da jini a jikinsu,” inji Hossam Abu Shahada, wanda ya shaida harin.
Asibitin Awda ya tabbatar da cewa ya karɓi gawarwaki 44, tare da 146 da suka jikkata. An kwashe masu rauni mafi tsanani zuwa wasu asibitoci a tsakiyar Gaza domin ceto rayukansu. Asibitin Al-Aƙsa Martyrs da ke birnin Deir al-Balah ya kuma ce ya karɓi gawarwaki 6 daga cikin waɗanda harin ya shafa.
Ma’aikatar Lafiya ta Gaza ta bayyana cewa daga ranar 7 ga Oktoba, 2023, lokacin da Isra’ila ta fara luguden wuta bayan harin Hamas, zuwa yau, Isra’ila ta kashe mutane 56,077, tare da 131,848 da suka jikkata. Daga cikin waɗannan, 5,759 sun rasa rayukansu tun daga ranar 18 ga Maris, bayan da Isra’ila ta kawo ƙarshen yarjejeniyar tsagaita wuta da ta ɗauki watanni biyu.
Ma’aikatar ba ta bambanta mayaka da fararen hula ba, amma ta ce fiye da rabin waɗanda suka mutu mata da yara ne.
Rundunar sojin Isra’ila, a martaninta ga tambayar da Associated Press ta aiko, ta ce tana nazarin rahotannin da ke cewa dakarunta sun yi sanadin mutuwar fararen hula. Ta ce tana harbi ne kawai a matsayin “gargaɗi” idan wasu na ƙoƙarin kusantar sansanoninta ta hanyar da ta kira mai barazana.
To, amma ƙungiyoyin agaji da shaidu sun musanta hakan, suna cewa harin kai tsaye ake yi kan jama’ar da ke neman abinci, a lokaci mafi muni da Gaza ke fama da karancin abinci da ruwa a tarihi.
Yayin da lamuran suka ƙara taɓarɓarewa, ƙungiyoyin agaji da dama na duniya sun buƙaci Isra’ila ta miƙa ragamar rabon agaji ga Majalisar ɗinkin Duniya (UN). Wasu daga cikinsu sun bayyana cewa tsarin da Isra’ila ke jagoranta ya gaza kuma yana ƙara jefa rayukan bayin Allah cikin hatsari.
Wata majiyar diplomasiyya daga Turai ta bayyana cewa, “idan duniya za ta rungumi yadda Isra’ila ke tafiyar da yaƙin Gaza, to za mu tunkari masifa mai girma fiye da tunaninmu.”
Masu sharhi sun ce wannan harin na Talata ya ƙara bayyana tsananin matsi da gazawar tsarin jin kai, inda mutum ke rasa ransa saboda ƙoƙarin samo abincin da zai ci da iyalansa.
“Mun fita neman abinci, amma muka dawo da gawar mijina.” Inji mahaifiyar Hamam Al-Farani, yayin da take kuka a gaban gawar mijinta, Alaa, wanda aka kashe tare da jikkata ɗansa.
Yayin da yawan mamata ke ci gaba da hauhawa a Gaza, da yawa daga cikin al’ummomin duniya suna tambaya: Shin akwai inda adalci ya fake? Shin akwai inda mafita ke farawa?
Amfanin agaji da duniya ke turawa Gaza ba ya isa, kuma tsarin rabawa na yanzu na ci gaba da barazana ga rayuka. Mutane da dama suna ganin lokaci ya yi da za a ɗauki matakin duniya don kare lafiyar jama’ar Gaza daga kisan kiyashi da yunwa mai hallakarwa.
