Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Nijeriya ta kasance ƙasa ta uku mafi ƙarfin soji a nahiyar Afirka, a cewar ƙididdigar ƙarfin soja na shekarar 2025.
Rahoton wanda ya yi nazari kan ƙarfin soja na ƙasashe 145 na duniya, ya sanya Nijeriya a bayan Masar da Aljeriya a nahiyar.
Matsayin, wanda VANGUARD ya ambata, yana amfani da alamomi sama da 60 don tantance ƙarfin sojan ƙasa. Waɗannan sun haɗa da yawan jami’an soji, bambancin tsarin makamai, kasafin tsaro, dabaru, da matsayi na yanki.
Masar ta ci gaba da riƙe matsayinta na babbar rundunar soji a Afirka, inda take matsayi na 19 a duniya, yayin da Aljeriya ke matsayi na 26.
Nijeriya ta hau matsayi na 31 a duniya, wanda ke nuni da ƙoƙarin da ake yi na haɓaka rundunonin soji da kuma ƙarfafa ayyukan tsaro, musamman a ayyukan yaƙi da ta’addanci da kuma saka hannun jarin tsaro.
Afirka ta Kudu, wadda aka taɓa ganinta a matsayi na ɗaya a sojan nahiyar, ta zo ta huɗu a Afirka kuma ta 40 a duniya. Habasha, Angola, da Maroko suma sun kasance cikin manyan ƙasashe 10 na soja na Afirka.
Manyan ƙasashen Afirka 10 Mafi ƙarfin Soji a 2025:
Misira ( Matsayinta a duniya: 19)
Algeria (26)
Nijeriya (31)
Afirka ta Kudu (40)
Habasha (52)
Angola (56)
Maroko (59)
Jamhuriyar Demokraɗiyyar Kongo (66)
Sudan (73)
Libya (76)
Manyan ƙasashe 10 na duniya mafi ƙarfin soja:Amurka
Rasha
Chana
Indiya
Koriya ta Kudu
Ingila
Faransa
Japan
Turkiyya
Italiya.
