Daga AISHA ASAS
Fitacciyar jarumar masana’antar Nollywood, Regina Daniels, ta fito a wani sabon fim mai taken “The Royal Assignment” wanda aka saki a YouTube ranar 24 ga Yuni. Fim ɗin ya ƙunshi salon sarauta da cin amana, inda Regina ke taka rawa a matsayin yarinya mai hangen nesa da hikima.
A cikin sa’o’i goma sha biyu kacal, fim ɗin ya samu sama da 300,000 ɓiews, tare da samun martani masu kyau daga masu kallo a sassan duniya.
