Rayuwar matafiya ’yan Arewa na cikin haɗari 

Spread the love

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Kasa da mako guda da kisan gillar da aka yi wa wasu matafiya su 12 da suka fito daga Zariya a Jihar Kaduna don zuwa ɗaurin auren ɗan uwansu a ƙaramar Hukumar ƙua’an-Pan ta Jihar Filato, an sake yi wa wasu matafiya ’yan Jihar Kano su biyu kisan gilla a Jihar Binuwai. Dukkansu kuma an kashe su ne don su musulmi ne ’yan Arewa, waɗanda suka samu kansu a wani yanki ba tare da sanin yanayin halin da wuraren suke ba.

Ga duk mai hankali da natsuwa ya san abin da aka yi wa matafiya a garin Mangun da ke cikin yankin ƙaramar Hukumar Mangu, abin Allah wadai ne da takaici. Kuma kamar yadda Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang ya faɗa, abin da ya faru rashin hankali ne da wauta.

Wannan ba shi ne karon farko da irin haka ke faruwa a Jihar Filato ba, jihar da ta jima cikin matsalar tsaro mai nasaba da addini da ƙabilanci. Idan ba a manta ba, a jihar ne aka kashe Janar Mohammed Idris Alƙali a shekarar 2018 a kan hanyar sa ta zuwa ganin iyalinsa a Jihar Bauchi. Haka ma a shekarar 2021 an kashe wasu matafiya musulmi su 22, akan hanyarsu ta komawa garinsu Ikare dake Jihar Ondo bayan sun fito daga taron Mauludi a Jihar Bauchi. Sannan akwai lokacin da wasu matasa da suka fito daga wajen taron Mauludi a Jos su ma aka hallaka su a hanyar komawa gida. Bayan nan, akwai wasu da suka fito daga ƙaramar Hukumar Ningi ta Jihar Bauchi, waɗanda su ma aka yi musu kisan gilla a garin Langtang da ke Jihar Filato.

An yi lokacin da hanyar Abuja zuwa Jos ta gagari matafiya Musulmi da ke hanyar zuwa jihohin su, a yankin Arewa maso Gabas, irin su Bauchi, Gombe, Adamawa da Taraba, domin yadda ake tsayar da motoci kan hanyar Riyom zuwa Jos ana binciken wane ne Musulmi don a kashe. Saboda mutanen ƙauyukan na zargin Fulani na kai musu hare-hare. Allah kaɗai ya san yawan mutanen da suka ɓata a wannan hanyar ko aka yi musu kisan gilla, saboda kawai su musulmi ne. Har yanzu wasu basu san inda ’yan uwansu suke ba, tun bayan da suka ji sun taso daga Abuja ko wata jiha daga kudancin ƙasar nan, za su bi ta Jos zuwa Arewa. 

ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a jihohin tsakiyar Nijeriya, irinsu Binuwai, Nasarawa, Kogi da Filato, na daga cikin dalilan da ke ƙara hassala waɗannan damuwoyi, kuma ya zama wajibi Gwamnati ta tabbatar an samu ingantaccen tsaro da zaman lafiya a yankin. Idan ba haka ba, akwai fargabar yankin da ya kasance mahaɗar Nijeriya zai iya komawa sanadin rabuwar ƙasar nan. 

Dukka waɗannan mutane da aka yi wa kisan gilla, babu wanda hukuma ta bi wa kadin zaluncin da aka yi masa. Ko da an yi wani abu bai wuce kama wasu da ake zargi, a kai su kotu, sannan daga baya a sake su saboda rashin ƙwararan hujjoji ko wasu dalilai. Daga nan kuma zance ya wuce, babu wanda ke sake cewa komai. Daga jami’an tsaro zuwa kan gwamnati, babu wanda zai ƙara fitowa ya ce ga matakin da ake, ko kuma ga abin da aka yi. Hatta game da kisan gillar da aka yi wa babban jami’in soja a yankin Du dake ƙaramar Hukumar Jos ta Kudu, jama’a har yanzu suna son su ji wanne hukunci aka yanke wa waɗanda aka kama da hannu a kisan gillar da aka yi masa.

Mutane da dama na ɗora alhakin cigaba da faruwar kisan gillar da ake yi wa matafiya da sunan ɗaukar fansa kan ƙalubalen tsaro da ke faruwa a Jihar Filato da wasu jihohin ƙasar nan, akan gwamnati, saboda a cewar su idan da gwamnati na ɗaukar tsauraran matakai da hukunta masu aikata wannan ɗanyen aikin, to da yanzu abubuwan sun yi sauƙi. Amma abin takaici shi ne, ana so a mayar da wannan ɗanyen aiki ya zama abin yayi, mutane na fargaba su biyo hanyar da suka san mazauna yankunan ba ’yan uwansu na addini ko ƙabilanci ba ne. Ko kuma suna fargabar taka sawun ɓarawo, su shiga wani yanki a lokacin da jama’a ke cikin alhinin faruwar wani al’amari na tsaro, don kar a huce a kansu da sunan ramuwar gayya.

Kamar yadda Gwamnan Jihar Filato ya faɗa bayan da ya je wajen da aka yi wa matafiyan Jihar Kaduna kisan gilla, inda ya ce mutanen yankin suna cikin baƙin cikin hare-haren ta’addancin, da mutanen da suke zargi Fulani ne, suke kai wa ƙauyukansu. Haka ma abin da ya faru a Jihar Binuwai da Jihar Edo, uzurin da ake bayarwa shi ne ’yan ta’addan da ake zargi Fulani ne sun addabi jama’ar yankunan, don haka duk inda aka ga Musulmi da siffar ’yan Arewa sai a kashe, don ɗaukar fansa. Subhanallah! 

Yanzu ya dace kenan, duk lokacin da aka samu aukuwar wani al’amari na harin ’yan ta’adda ko kashe-kashe sai a hau tare hanya ana yi wa matafiya da basu san hawa ba basu san sauka ba, kisan gilla, don kawai sun fito yanki ɗaya da waɗanda ake zargin su ne suka aikata laifin. Wannan rashin hankali ne kuma dabbanci ne, babu inda dokar ƙasa da zamantakewa ta hankali suka lamunci haka a duniya. Sannan ci gaba da barin hakan na faruwa ganganci ne ga zaman lafiya da tsaron ƙasar nan.

Yanzu kenan ya nuna babu inda ɗan Arewa zai shiga ya sake da rayuwarsa cikin aminci idan ba a Arewa ba ko jihar da ya fito. Ba tun yanzu ba, muna ganin irin wulaƙancin da ake yi wa ’yan Arewa da ke tsallakawa jihohin Kudu ko Gabashin ƙasar don kasuwanci, inda ake hallaka su da dukiyarsu ko a ƙuntatawa rayuwarsu, saboda kawai su ’yan Arewa ne! Kai ka ce ana cikin yaƙin basasa. Alhalin su mutanen da suke wannan rashin hankalin suna da ’yan uwansu dake zaune a Arewa cikin aminci da kwanciyar hankali babu wanda ke takura musu ko cutar da su da sunan su ba ’yan Arewa ba ne, saboda mun yarda dukkan mu ’yan Nijeriya ne.

Lallai ne Gwamnatin Tarayya da ta jihohi su tashi tsaye haiƙan don ganin an kawo ƙarshen wannan rashin hankali da ke faruwa, domin shirun su da rashin hukunci babban kuskure ne da nan gaba zai iya raba ƙasar ko kawo rashin tsaro mafi muni a ƙasar nan. Idan har za a cigaba da ware ’yan wani sashi na ƙasa ana yi musu kisan gilla, don kawai su musulmi ne ko ’yan Arewa.

Yaushe a ƙasar nan talaka ya gama da batun ƙalubalen rashin kyan hanyoyi, matsalar ’yan bindiga masu satar mutane da ’yan fashi, da har za a jefa shi cikin barazanar rasa rayuwarsa a lokacin da yake kan hanya, don neman abin da zai rufawa kansa asiri da iyalansa, ko kuma wata hidima ta rayuwarsa.

Lallai a fahimci kowanne rai yana da muhimmanci, da ran Musulmi da na Kirista, da ran ɗan Arewa da na Kudu. A bai wa kowanne ɗan Nijeriya tsaro da muhimmanci, sai a zauna lafiya da juna. Kada gwamnati ta riƙa yin shiru ko ta kawar da kai, daga irin waɗannan abubuwa da ke da tasiri wajen haɗawa ko raba kan al’ummar ƙasar nan.

Muna addu’ar Ubangiji Allah Ya karɓi shahadar waɗanda aka yi wa kisan gilla ba da haƙƙi ba. Ya bai wa iyalansu da ‘yan uwansu haƙurin jure wannan babban rashi da aka yi mana bakiɗaya. Ya kuma dawo mana da tsaro akan hanyoyinmu, da garuruwanmu. Amin

By ukarofi