
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Bayo Onanuga ya ce babu wani sauyi da aka yi a muƙamin Sakataren Gwamnatin Tarayya, wanda Sanata George Akume ya ke riƙe da shi.
A sanarwar da ya fitar ranar Asabar, Onanuga ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu, wanda a yanzu ya ke ƙasar Saint Lucia, bai yi kowane sabon naɗin muƙami ba, don haka babu batun sauyin.
Ya kuma ce, labarin da ake yaɗawa na cewa an maye gurbin Akume, ba gaskiya bane, saidai abu ne da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da al’umma.
Haka kuma, Fadar Shugaban Ƙasar ta shawarci ƴan Nijeriya da su yi watsi da labarin ƙaryar, wanda a cewarsa babu ƙamshin gaskiya a cikinsa.
