
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An sake ganin Ministan Abuja Nyesom Wike da dakataccen Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara a inuwa ɗaya tun bayan da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranci sulhunta su a makon da ya gabata.
A yayin jana’izar kawun Wike a garin Rumuepirikom na Ƙaramar Hukumar Obio/Akpor a jihar ne aka gansa da Fubara da dakataccen Kakakin Majalisar Dokoki na Ribas, Martins Amaewhule, ranar Asabar.
Ƴan siyasar uku sun shafe kusan shekaru biyu suna rikicin siyasa a tsakaninsu.
Ganin su a tare ya biyo bayan ganawa da suka yi da Shugaba Tinubu a Faɗar Shugaban Ƙasa dake Abuja, lamarin da ake ganin ya kawo ƙarshen rikicin siyasar jihar.
Duk da cewa babu wani tsokacin siyasa a taron, ganin su a waje ɗaya ya nuna cewa akwai yiwuwar dokar ta-ɓaci da aka sanya a jihar ta zo ƙarshe.
Haka kuma, Kakakin Wike, Lere Olayinka ya yaɗa wani bidiyo da ke nuna Fubara a gidan Wike na Fatakwal, Babban Birnin Ribas.
