“Matasa a dage a nemi sana’a a daina ɓata data ga banza”
Daga UMAR GARBA, a Katsina
Khadija Nura Batsari da aka fi sani da Umnoorthrifts, ma’aikaciyar gwamnati ce kuma matashiyar ‘yar kasuwa da ke amfani da shafukan sada zumunta don bunƙasa harkokin kasuwancinta.
Wakilin Blueprint Manhaja a Katsina Umar Garba, ya tattauna da Khadija Umnoorthrifts game da batutuwan da suka shafi dabarun tallata kasuwanci a kafofin sada zumunta, ba wa matasa maza da mata shawara a kan su dogaro da kansu don su zamo masu amfani ga al’umma, nasarori da kuma ƙalubalen da ta fuskanta kafin ta taka matakin da take a kai yanzu da dai sauran batutuwa. A sha karatu lafiya.
MANHAJA: Za mu so ki gabatar da kanki ga masu bibiyarnu.
KHADIJA: Sunana Khadija Nura Batsari da aka fi sani da Umnoorthrifts a shafukan Soshiyal Midiya.
Za mu so jin taƙaitaccen harihinki?
Ni dai sunana Khadija Nura Batsari kamar yadda na faɗa, an haife ni a shekarar 1996 cikin Jihar Katsina. Na yi primary a Usman Nagogo Memorial Primary School daga shekarar 2000 zuwa 2006, na yi karatun secondary a Kiddies International School daga 2006 zuwa 2012 daga nan sai na shiga jami’ar Umaru Musa Yar’adua Uniɓersity da ke Katsina, daga 2013 zuwa 2007, na yi hidimar ƙasa a shekarar 2018. Bayan na kammala digiri na farko na sake komawa karatun digiri na biyu inda na gama a shekarar 2022.
Shin ke ‘yar kasuwa ce ko kuma ma’aikaciyar gwamnati?
Ina aikin gwamnati kuma ina kasuwanci. Na fara aikin gwamnati a asibitin koyarwa ta gwamnatin tarayya da ke nan Katsina, wato Federal Teaching Hospital Katsina, a shekarar 2021. To bayan na haihu sai naga yadda kayan yara ke tsada kuma da an saya sai su yi kaɗan. Wannan ya saka min sha’awar neman kayan yara masu kyau a farashi mai sauƙi. Wannan ne dalilin da ya kai ni ga fara sana’ar sayar da kayan yara ɗin.
An fi saninki a harkar kasuwanci. Ta wacce hanya kika tallata sana’arki cikin ƙanƙanin lokaci mutane suka san me kike sayarwa?
Na fara tallata kasuwanci na ta hanyar amfani da WhatsApp kaɗai a lokacin ‘yan uwa da abokan arziƙi kawai nake sayar wa kaya, daga baya sai na shiga ‘Online Classes’ na koyon kasuwanci waɗannan ‘Classes’ sun buɗe min ido kan kasuwanci daga nan ne na gane kasuwanci ya fi wuce ka tsaya kana sayar wa ‘yan uwa da abokan arziƙi kaya su kaɗai wato ba kawai ka tsaya sayar da kayanka a soshiya midiya ba kaɗai, da haka na fara koya ina yi kaɗan kaɗan. Alhamdulillah inada followers (mabiya) kusan dubu 12 yanzu haka a Tiktok da kuma Instagram kuma dukkansu masu sayan kaya ne daga waje na.
Alhamdulillah!
Kwanakin baya mun ji shafin Northern Hibiscus da ke a manhajar Instagram ya zaɓe ki a matsayin gwarzuwar ‘yar kasuwa ta watan Afrilu 2025. Shin me ya sa masu tafiyar da shafin suka zaƙuloki a cikin dubban mata ‘yan kasuwa na Arewa?
Ta hanyar jajircewa da kuma addua duk abinda kasa gaba idan har ka daure ka jajirce kuma kabi da addu’a, komi yana zuwa da sauƙi da yardar Allah.
Haɗa kasuwanci da kuma aikin gwamnati gami da kula da iyali ga mata ba abu ba ne mai sauƙi. Ta ya sana’arki ta shafi kula da gida ko kuma iyalinki?
Gaskiya kam haɗa iyali da aikin gwamnati da kuma sana’a da wahala sosai, amma idan ka tsara komai ka ba wa kowane aiki daga ciki lokacinsa komi yana zuwa da sauƙi. Alhamdullih!
nakan fitar da lokacin jera sabbin kaya da lokacin ɗaukar kayan hoto sannan ina da masu taya ni wannan aiki, duk ranar da za’a yi hoto akwai mai ɗuwa ta kama ayi haka duk ranar da za’a a buɗe sabbin kaya. To idan ka tsara irin haka sai komi yake zuwa da sauƙi. Alhamdullih!
Mata da yawa na son fara kasuwanci ko wata sana’a amma jari ne matsalarsu. Ta wacce hanya zasu samu jarin farawa?
Hanyar ita ce su fara da ƙaramin jari idan ka ce sai ka tara kuɗi zaka fara wata sana’a sai a hankali, amma idan kana da ‘yan kuɗinka koda kaɗan ne ka fara da shi idan ma babu kar ki jira, mutane dayawa na yin ‘dropshopping’ kuma suna samu sosai kowa da aka gani akwai inda ya fara.
Wacce shawara zaki bai wa matasa maza da mata akan su rungumi sana’o’i su daina zaman banza?
Rayuwa ta yi tsada, kuma sana’a ita ce mafita yanzu kar ka ce sai kana da jari, kar ka ce jarinka kaɗan ne ka fara da ɗan kaɗan da kake da shi saboda, kowa ka ji labarinsa zaka ji da kaɗan kaɗan ya fara. Shawara ita ce matasa a dage a nemi sana’a a daina ɓata data haka nan, a kama sana’a don rufa wa kai asiri.
Me ye burinki a nan gaba?
Buri na yanzu na buɗe babban shago na zahiri inda za a iya zuwa a saya kaya tunda yanzu a kafafen sada zumunta na ‘online’ kaɗai muke sayar da kaya.
Ko zaki faɗa wa masu bibiyarnu nasarar da kika samu a harkokinki na kasuwanci?
Nasara kam Alhamdulillah! na haɗu da mutane da yawa ta haryar kasuwanci na waɗanda yanzu sun zama kamar ‘yan uwa ina godiya gare su, Alhamdulillah kuma na samu kuɗi (dariya..) na yi suna sosai, Umnoor na samun karɓuwa a wajen mutane daga jihohin Najeriya.
Duk inda aka samu nasara akwai yiwuwar an fuskanci ƙalubale kafin nasarar. Wane ƙalubale kika fuskanta tun bayan fara kasuwanci?
ƙalubale na farko an damfare ni sai da na gama haɗa kuɗin dila na tura wa wani mutum, ai kuwa mutumin nan yayi blokin ɗina, ba kuɗi ba kaya hakan ya janyo wa store ɗina na Umnoorthrifts babban koma baya. To Alhamdulillah ina aiki aka samu aka ƙara haɗa wani jarin aka cigaba.
Mun gode sosai da wannan dama da kika bamu don yin hira da ke.
Ni ma nagode sosai.
