Kotu ta ci tarar rundunar sojojin Nijeriya miliyan N50 saboda kisan direban tasi

Spread the love

Daga HABU ƊAN SARKI a Jos

Wata Babbar Kotun tarayya da ke zama a Jos ta zartar da hukunci kan shari’ar da ke gabanta game da ƙarar da iyalin wani direban tasi Sadiq Adamu suka shigar suna ƙalubalantar kisan da wasu sojoji suka yi masa, sakamakon azabtar da shi da suka yi a lokacin da yake hannun su.

A ƙarar da suka shigar mai lamba No: FHC/J/CS/35/2021, matar marigayin Sa’adatu Sabiu da wasu ta hannun lauyansu Barista M.S Salihu, sun ƙalubalanci rundunar sojojin Nijeriya da wasu biyu game da abin da suka kira, zalunci da tauye haƙƙin ɗan Adam.

Da take yanke hukunci ga wannan shari’a da ta ɗauki tsawon shekara uku ana fafatawa, Mai Shari’a Sharon T. Ishaya, ta zargi jami’an sojojin da suka azabtar da shi da laifin ƙin kai shi asibiti, bayan da suka lura da halin da yake ciki sakamakon azabtarwar da aka yi masa.

Ta ce, duk da kasancewar babu wata shaida da ta nuna rahoton ƙwararren likita game da musabbabin mutuwar tasa, amma tabbas yanayin da ya mutu ya nuna azabtarwar da aka yi masa ce ta hallaka shi.

Idan za a iya tunawa dai a an kama Sadiq ne wanda yake direban tasi ne a cikin garin Jos, a shekarar 2021 a yankin Farar Gada yayin da yake gudanar da aikinsa na ɗaukar fasinja, a lokacin akwai dokar hana zirga-zirga daga ƙarfe 10 na dare, sakamakon halin rashin tsaro da garin yake ciki a lokacin.

Iyalinsa sun yi zargin bayan da sojojin suka tafi da shi wajen su an azabtar da shi, har sai da rai ya yi halin sa. Ko da yake rundunar sojojin ta ƙaryata wannan zargi a farko, inda ta ce Sadiq ya rasa ran sa ne a gida gaban iyalinsa, kuma ya samu raunuka ne sakamakon dukan da jama’ar gari suka yi masa lokacin da aka zarge shi da yunƙurin da yi wa wata mata fyaɗe.

Iyalin marigayin sun nemi kotu ta tilasta rundunar sojojin ta biya su diyyar Naira Miliyan 250, saboda yunƙurin ɓata suna da cin zarafin sa da aka yi. Sai dai kotu ta yanke hukuncin tarar Naira Miliyan 50 ga rundunar sojojin, tare da jaddada cewa, kama mutumin da ake zargi da karya doka ba aikin sojoji ba ne, aiki ne na ýan sanda.

Da yake magana bayan wannan hukunci da kotu ta yanke, lauyan masu ƙara Barista M.S Salihu ya yabawa Kotun bisa hukuncin da ta yanke, tare da tunatar da jami’an soji su riƙa tsayawa akan aikin da doka ta basu damar yi, don kaucewa cin zarafi da tauye haƙƙoƙin ɗan Adam.

Ɗaya daga cikin ýan’uwan marigayin, kuma ɗan gwagwarmaya, Malam Aliyu Karafa ya yi godiya ga duk waɗanda suka taimaka musu wajen samun nasara akan wannan shari’a, tare da ƙarfafa gwiwar sauran ýan Nijeriya su daina jin tsoron neman haƙƙin su a gaban kotu, matuƙar sun san suna da gaskiya, kuma sun tanadi hujjojin da za su ba su nasara a gaban shari’a.

By ukarofi