Ku yi amfani da basirarku don samun sauyi ingantacce – Gwamna Lawal

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya buƙaci masu yiwa ƙasa hidima da aka turo Jihar Zamfara da su yi amfani da basirarsu don samun canji mai kyau a cikin al’ummar da suke zaune.

Gwamna Lawal yayi wannan kira ne a jawabin da ya gabatar a yau Talata a wajen wani muhimmin biki na rufe gasar Batch A Stream II Orientation Course na shekarar 2025 a Jihar Zamfara.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishinan matasa da wasanni Hon. Tasiu Musa Shinkafi ya ba da tabbacin cewa gwamnatin sa za ta tallafa wa mambobin ƙungiyar masu yiwa ƙasa hidima tare da samar musu da muhallin da za su iya gudanar da ayyukansu.

Gwamnan ya buƙaci ’yan ƙungiyar da su yi amfani da darussan horon da suka samu, tare da aiki da jajircewa a wuraren aikinsu na farko.

Gwamna Lawal ya cigaba da bada tabbacin cewa za a bai wa fitattun ‘yan ƙungiyar kyauta a ƙarshen hidimar a wani ɓangare na shirye-shiryen gwamnatin sa na zaburar da ‘yan ƙungiyar.

“Gwamnatin Jihar Zamfara tana martaba nagarta da ƙirƙire-ƙirƙire. Mun himmatu wajen karramawa tare da bai wa ‘yan ƙungiyar haɗin gwiwa da suka bambanta ta hanyar yin ayyuka da suka yi fice, da ayyukan ci gaban al’umma, da kuma kyawawan halaye a cikin wannan shekarar hidima, don haka wannan zai zama abin ƙwazo a gare ku don tunkarar shekarar hidimar ku tare da himma da himma mai ɗorewa”, in ji shi.

A nasa jawabin, kodinetan NYSC na Jihar Zamfara, Mallam Muhammad Lawan Ahmed ya yabawa ‘yan ƙungiyar bisa haɗin kan da suka bayar a tsawon makwanni uku da suka gabata.

Mallam Ahmed ya yi kira ga ’yan ƙungiyar da su tunkari mataki na gaba na hidimar cikin himma, gaskiya, da ƙwarewa.

Ko’odinetan ya yi amfani da wannan dama wajen miƙa godiyarsa ga Gwamna Dauda Lawal kan yadda gwamnatin sa ke tallafa wa hukumar NYSC da kuma samar da yanayi mai kyau don samun nasarar kwas ɗin Orientation.

Ko’odinetan ya buƙaci a samar da ingantattun ababen more rayuwa a sansanin ‘Orientation Camp’ domin sauƙaƙa wa masu yiwa ƙasa hidima da aka tura jihar.

Jaridar Blueprint Manhaja ta rawaito cewa babban abin da ya fi ɗaukar hankali a wajen bikin shi ne bayar da lambar yabo ga kwamishinan matasa da wasanni Hon Tasiu Musa Shinkafi da kuma jami’an sansanin da suka yi fice a lokacin aikin wayar da kan jama’a.

By ukarofi