Sakatarori sun shiga ofis a Kebbi 

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi 

Ranar Larabar da ta gabata ne dukkanin sababbin  Sakatarori da aka naɗa suka shiga ofisoshinsu don kama aiki a jihar Kebbi.

Idan dai ba a manta ba kwanakin baya ne gwamantin jihar Kebbi ƙarƙashin jagorancin Malam Nasir Idris ta sauke dukkan sakatarorin ƙananan hukumomi ashirin da ɗaya da ke faɗin jihar tare da maye gurabunsu da sababbi, sai dai ba su kama aiki ba kamar yadda gwamnatin jihar ta bayar da umarni sai bayan ta kammala waɗansu shirye-shirye da ta ke yi.

Malam Muhammed Tsalhatu Bubuche shi ne sabon Sakataren ƙaramar hukumar mulki ta Augie ya bayyana cewa shi daman tsohon ma’aikaci ne saboda haka ba ya sa ran ya tarar da wani sabon abu sai dai ya nemi haɗin kai daga al’umma musamman ma’aikatan ƙaramar hukumar mulki ta Augie don kawo cigaba.

Ya kuma alƙawarin bayar da gudummawa wajen ganin an samu nasarori saboda haka a ko da yaushe ƙofar su a buɗe ta ke don karɓar shawara ko kuma ƙorafi daga ko’ina tare da ɗaukar ƙwararan matakai a matakin ƙaramar hukuma kuma ida abin ya gagare su za su kai ga matakin jiha musamman saboda gwamna mutum ne da ke da kunnuwan sauraren al’umma.

Da ya ke jawabi shugaban ƙaramar hukumar mulki ta Augie Honarabul Yahaya Muhammed Augie ya yaba wa Gwamna Malam Nasir Idris bisa ga tunaninsa na zaƙulo waɗanda ke da sani musamman a harkar ƙananan hukumomi.

Ya kuma yi alƙawarin aiki tukuru tare da baiwa sabon Sakataren haɗin kai don samun cigaban ƙaramar hukumar mulki ta Augie da kuma jihar Kebbi bakiɗaya.

By ukarofi