NULGE ta yi kira ga ‘ya’yanta a Jihar Katsina su koma gona

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Ganin yadda zaman lafiya ya fara samuwa a wasu ƙananan hukumomi da suka yi ta fama da matsalar ta’addanci, shugaban ƙungiyar ma’aikatan ƙananan hukumomi a Jihar Katsina kwamred Nasiru Wada Mai’adua ya shawarci ya’yan ƙungiyar da su rungumi harkar noma a yankunan su.

Shugaban ƙungiyar na magana ne da manema labarai a ofishin sa da ke garin Katsina.

Ya ce yawancin ma’aikatan ƙananan hukumomi a jihar sun fi yawa a karkara “Yakamata waɗanda basa noma da su sake tunani,”inji kwamred Wada Mai’adua.

“Ta wannan ne kawai ma’aikaci zai iya wadata iyalan sa da abinci har ma ya sami abin hidimar yau da kullum na iyali,”kwamred Mai’adua ya ce.

Shugaban ƙungiyar ya bayyana cewa lokaci yayi da ba ma ma’aikacin ƙaramar hukuma ba duk wani ma’aikacin gwamnati da ya tashi tsaye wajan neman wata sana’a bayan ya tashi aikin gwamnati.

Ya kuma yabawa gwamnatin Dikko Raɗɗa kan ɓullo da shirin rumbun hatsi a ƙananan hukumomi 34 da ke jihar.

Kwamred Nasiru Wada ya ce wannan shiri zai sauƙaƙa wa ƙananan ma’aikata a ƙananan hukumomi wajen wadata iyalan su da kayan abinci wanda ya zama tagomashi.

Sai yayi kira ga malam Dikko Raɗɗa da ya ƙara da su gero,wake,masara da sauran su cikin hatsin da ake saidawa ma’aikatan cikin farashi mai rangwame.

By ukarofi