Yadda tsofaffin ɗaliban aikin jarida na Legal suka gudanar da taronsu a Kano

Spread the love

Daga AISHA ASAS

An jaddada buƙatar ƙungiyoyin tsoffafin ɗalibai da su ƙara jajircewa wajen bai wa makarantunsu
gudunmawa domin cigaban su.

Shugaban sashin kula da harkokin tsoffafin ɗalibai kwalejin Koyon Nazarin harkokin Addinin Musulunci da Shari’a ta Mallam Aminu Kano (Director Aluminum) Mallam Aminu Gabari ya jaddada hakan a lokacin taron Ƙungiyar tsofaffin ɗaliban nazarin koyan aikin jarida na Kwalejin ajin 2014.

Yace la’akari da yadda makarantar ta yaye dubunnan ɗalibai shekaru 49 da suka gabata, akwai buƙatar baiwa makarantar gudunmawa.

Mallam Aminu Gabari ya yabawa ƙoƙarin ƙungiyar tsoffin ɗaliban ajin bisa kafa ƙungiyar tare da buƙatar su ƙara jaddada haɗin kai da taimakon juna.
Shugaban yayi amfani da taron wajen lasafta aiyyukan da gwamnatin Kano ta samar a kwalejin da suka haɗar da gyaran katafaren ɗakin taro a kwalejin da ya kai Naira Milyan 40 da sauran gine gine.

Da yake nasa jawabi, Sakataren Ƙungiyar tsoffin ɗaliban, Comrade Ibrahim Hamisu, yace suna gudanar da taron ne duk shekara domin sada zumunci da bijiro da hanyoyin taimakon juna domin cigaban tsoffin ɗaliban da ma Kwalejin ta Legal.

Ya yabawa tsoffafin ɗaliban bisa halattar taron, sannan ya yi kira gare su da su zama jakadu nagari wajen aiwatar da aikin jarida da zai taimaki rayuwar al’umma.

Wakiliyarmu ta ruwaito cewa taron ya samu halattar ƴayan ƙungiyar tare da tattauna mahimman batutuwa da suka jiɓanci Ƙungiyar.

By ukarofi