Daga USMAN KAROFI a Abuja
Rikici ya ɓarke a kasuwar Gosa da ke kan titin filin jirgin sama a ƙaramar hukumar birnin tarayya (AMAC) a ranar Juma’a, sakamakon kisan wani makiyayi da aka ce sunansa Saleh Aliyu. Rahotanni sun bayyana cewa wasu mutane sun kai masa farmaki da adda yayin da yake hutawa a kasuwa a daren Alhamis, sannan suka jefar da gawarsa kusa da wani rafin da ke unguwar.
Wani mazaunin yankin mai suna Yohana Joseph ya shaida cewa rigima ta fara ne tun makonni da suka gabata tsakanin makiyayin da ɗaya daga cikin masu tsaro a kasuwar. A cewarsa, “Sun taɓa samun saɓani da Fulanin a baya. Amma ranar Alhamis suka same shi a kasuwa, suka yi masa duka da adda, suka ɗauke gawarsa suka jefar kusa da ruwa.” Yohana ya ƙara da cewa waɗanda ake zargin sun je suka bayyana laifinsu ga iyalan mamacin, wanda hakan ya tayar da hankali sosai a ranar Juma’a.
A safiyar Juma’a, iyalan mamacin da sauran makiyaya sun iso kasuwar ɗauke da adduna da wasu makamai, suna neman ramako. Wannan lamarin ya haddasa ruɗani a kasuwar, inda ‘yan kasuwa da abokan hulɗa suka tsere domin tsira da rayukansu. Sai da jami’an tsaro suka isa wajen kafin aka samu daidaito. Bayan haka, gawar Saleh Aliyu an kai ta gida an binne shi kamar yadda al’ada ta tanada.
Kwamishinan ‘yan sandan babban birnin tarayya, Saka Ajao Adewale, ya tabbatar da faruwar lamarin yayin taron manema labarai a ranar Juma’a. Ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa kuma suka hanzarta zuwa domin shawo kan lamarin. “Abin ya faro ne daga zargin satar doya, wanda wani ya ɗauki doka a hannunsa ya kashe wani mutum cikakke,” in ji CP Adewale. Ya ce yanzu haka an kama mutum shida da ake zargi da hannu a cikin lamarin kuma suna hannun ‘yan sanda.
Kwamishinan ya ce suna aiki tare da shugabannin al’umma da sarakunan gargajiya domin kwantar da hankali da hana ɓarkewar wani rikici. A cewarsa, an samu daidaito a kasuwar, kuma jami’an tsaro na ci gaba da sintiri don tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.
