
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar kula da Yanayi ta Ƙasa (NiMET) ta ce ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama haɗe da tsawa daga ranar Litinin zuwa Laraba a faɗin Nijeriya.
A saƙon hasashen da ta fitar a Abuja, NiMET ta ce akwai yiwuwar samun hadari da tsawa a safiyar ranar Litinin a wasu yankunan Jihohin Taraba da Adamawa.
Haka kuma, za a samu ruwan sama da tsawa a jihohin Zamfara, Adamawa, Kebbi, Taraba da Kaduna a yammacin Litinin.
A shiyyar Arewa ta Tsakiya kuwa, ta yiwu a samu yayyafi da tsawa a wasu yankunan jihohin Abuja, Kogi, Neja, Benuwai, Filato da Nasarawa da sa’o’in rana da yammaci.
A kudu, yanayin ka iya zuwa ɗauke da hadari da ruwan sama da safe a jihohin Legas, Ogun, Ondo, Akwa-Ibom, Kuros-Riba, Ribas, Delta da Bayelsa.
NiMET, hallau ta ce a yammacin Litinin ɗin ne ake sa ran samun yayyafi a yankunan Oyo, Ondo, Ekiti, Osun, Ogun, Imo, Abia, Edo, Ebonyi, Enugu, Legas, Akwa-Ibom, Kuros-Riba, Delta da Bayelsa.
A ranar Talata kuma, ana sa ran samun rana da ɓurɓushin hadari a Arewacin Nijeriya da safiya, kamar yadda hukumar ta sanar.
Har’ilayau, ta yi hasashen samun tsawa da ruwan sama a yankunan Sakkwato, Kebbi, Kano, Katsina, Kaduna, Taraba, Adamawa, da Zamfara a yammacin ranar Laraba.
Daga ƙarshe, ta yi kira ga al’umma da ta ɗauki matakan kariya duba da cewa akwai yiwuwar a samu iska mai ƙarfi a yankunan da ka iya samun tsawa.
