Ga fatawa kan batun masu ƙwacen waya

Spread the love

Daga ABDULLAHI JIBRIL DANKANTOMA

Ga ɗan ƙaramin taimako da zan iya bayarwa game da masu ƙwacen waya, amma idan ku na nesa ba gab da gab ba tunda mun zama matsorata, da an gan su sai a fara gudu rudu-dudu a runtuma, wannan na bangazar wannan, wancan na bangazar wancan, ba maza! ba mata! ba matasa! ba dattijai! kowa sai ya ranta a na kare. 

Ashe da zamanin da ake yaƙi muka zo da ba za mu iya fita filin daga ba a fafata da mu. 

An dai ji jiki wani lokacin. Ka ga masu mota na juyawa suna ribas, masu mashin mai ƙafa biyu na juyawa da gudu, masu Adaidaita Sahu su ma suna juyawa da gudu, masu keke da ƙafa su su na ƙoƙarin hankaɗe junansu.

To, akwai dabarar da muka kasa yi ko tunawa ta ragwaye irinmu gabaɗaya. 

Kowa ya mallaki ‘touch light’ ya zuba mata sabon batir. Idan har muka hango su sai kowa ya kunna tasa a dallare musu idanunwansu. Wallahi za su kiɗime su ga duhu. Sai wasu daga cikin jarumin cikinmu su yi kansu, babu abinda za su iya yi a wannan lokacin a faɗa su da duka, a ƙwace makamansu.

Idan kuma misali mutum shi ɗaya ne su kuma su biyu za ka iya saurin kunna ‘touch ligh’ ɗinka ka dallare musu idanu duk su biyun. Idan za ka iya afka musu da hauri da ƙafa ko kutufo sai ka yi. Idan kuma kai rago ne sai ka ranta a na kare. 

Wannan siririn ko jami’an tsaro na basu shi zasu iya jarrabawa wajen kama su ko kama ’yan shayeshaye a maɓoyarsu da dare.

A zamanin da ana amfani da haske ne wajen kama ɓarawo ko wata muguwar dabba. Hatta maciji idan ka dallare masa ido da ‘touch light’ yana kiɗimewa duk da hasken idanuwansa. 

Shi ya sa a da za ka ga masu tafiyar dare suna ɗaukar fitila tun ma kafin zuwan ‘touch light’ har kuma ta zo Fulani suke amfani da ita a daji wajen haske hasken miyagun ƙwari da namun daji. 

A jarraba wannan fatawar tawa. Kuma don Allah a yaɗa wannan rubutun har kowa ya karanta ko a karanta a ba shi labari, don al’ummar Musulmi su amfana da wannan fatawar tawa. 

Dankantoma, wanda ake yi wa laƙabi da Uncle Larabi, marubuci ne a Kano. Za a iya samun sa a wannan lambar waya 08065418892

Juma’a, 13 ga Yuni, 2025

By ukarofi