
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Alhamis ne Kotun Ƙoli ta tabbatar da Monday Okpebholo na jam’iyyar APC a matsayin zaɓaɓɓen gwamna a Jihar Edo, lamarin da ya kawo ƙarshen shari’ar da aka ɗauki watannin a kai tun bayan zaɓen da aka gudanar a Satumban 2024.
A wani hukunci na tawagar alƙalai biyar ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Garba, kotun ta yi watsi da ƙarar da babbar jam’iyyar adawa (PDP) mai ɗan takara Asue Ighodhalo ta ɗaukaka a wajenta, tana mai cewa ta ɗauki matakin ne duba da cewa ƙarar ba ta da nagarta.
Mai Shari’a Garba ya bayyana cewa, waɗanda suka shigar da ƙarar sun gaza samar da gamsassun hujjoji da za su tabbatar da cewa Okpebholo bai ci zaɓen gwamnan ba.
Haka kuma, ya ce PDP da ɗan takararta sun gaza gamsar da kotun game da cewa hukuncin da majalisar ƙorafin zaɓe ta jihar da Kotun Ɗaukaka ƙara suka yi ba su inganta ba, don haka alƙalin ya yi watsi da ƙarar tasu.
Hakan ya biyo bayan ƙalubalantar ayyana Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan da PDP ta yi, inda ta kafa hujja da cewa akwai haramtattun ayyuka da aka yi yayin gudanar da zaɓen, lamarin da ya sa ta nemi a soke sakamakon.
Da fari dai majalisar ƙorafin zaɓen da Kotun Ɗaukaka Ƙara sun yi watsi da ƙorafin na PDP, lamarin da ya kai jam’iyyar zuwa Kotun Ƙoli domin neman a yi hukunci na ƙarshe akan zaɓen kamar yadda dokar ƙasa ta tsara.
