Yadda Adoke ya dakatar da Jonathan tsige ni a gwamnan Borno – Shettima

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bayyana cewa, saura ƙiris a cire shi a matsayin gwamnan Jihar Borno a zamanin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Johnathan, inda ya yi nasarar tsira daga hakan ta hannun Antoni Janar na Ƙasa na lokacin, Mohammed Bello Adoke.

Shettima, wanda ya yi gwamna a Jihar daga 2011 zuwa 2019 ya faɗi haka ne a ranar Alhamis a Abuja, yayin taron gabatar da jawabin wata takarda da tsohon antonin ya rubuta mai suna ‘OPL 245: Inside Story of the $1.3 Billion Nigerian Oil Block’.

Mataimakin Shugaban Ƙasar ya ce, akwai shirin tsige shi daga muƙaminsa na lokacin ba bisa doka ba, amma Adoke ya tirje da shaida wa Shugaba Goodluck cewa ba shi da ikon yin hakan a dokane na ya cire ko da kansila ne ballantana gwamna.

A lokacin, fitinar Boka Haram ta yi ƙamari a Borno inda ta jefa jihar da al’umma cikin mawuyacin hali, lamarin da ya jefa Shettima cikin matsi daga tarayya bisa taɓarɓarewar tsaro.

A watan Disambar 2011 ne Jonathan ya sanya dokar ta-ɓaci a wasu sassan Borno da Filato. Zuwa Mayu, 2013 ne aka faɗaɗa dokar ta mamaye sauran sassan jihohin Borno, Yobe da Adamawa.

Akan haka ne Adoke ya yi amfani da ƙarfin doka wajen hana Shugaba Jonathan tsige kowane ɗaya daga cikin gwamnonin jihohin matuƙar ba su saɓa wa dokar ƙasa ta 1999 ba.

Shettima ya bayyana hakan ne a sakamakon tafka mahawara da al’umma ke yi akan sanya dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a Ribas a rana 18 ga watan Maris, 2025.

By Babaji