Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata kotun tarayya da ke birnin Ottawa na ƙasar Kanada ta hana Iyanbe Eriator, tsohon jami’in Hukumar Yaƙi da ’Yan Fashi da Makami (SARS) na rundunar ‘yan sandan Nijeriya zama ɗan ƙasarya saboda alaƙarsa da rundunar da ake zarginsa da cin zalin ’yan Nijeriya.
Eriator, wanda ya shiga Kanada ba bisa ƙa’ida ba ta kan iyakokin ƙasa daga Amurka a watan Oktoban 2017, ya garzaya kotu don neman takardar zama ɗan wasa bisa shari’a, bayan Hukumar Shige da Fice da Kula da ’Yan Gudun Hijira ta Kanada (IRCC) ta hana shi zama na ɗan ƙasar.
Sai dai a cewar Peoples Gazette, Mai Shari’a Yvan Roy na Kotun Tarayya ta Kanada, a hukuncin da ya yanke, ya ce Eriator ba shi da izinin shiga Kanada saboda alaƙarsa da ‘yan sandan Nijeriya a baya.
Alƙalin ya ce ‘yan sandan Nijeriya na tabon yi w ’yan Nijeriya fyaɗe, cin zali, gallazawa, bautar da su, ɓatar da mutane, da kuma kashe ‘yan ƙasa, inda ya ƙara da cewa duk waɗannan sun saɓa wa dokar Rome kan laifukan cin zarafin bil’adama.
“Mista Eriator, a matsayinsa na memba na ‘yan sanda, yana da hannu wajen aikata laifukan saboda ba zai iya cewa bai taɓa aikata ta’addanci ko azabtarwa ba,” inji alƙalin na Kanada.
“Kasancewar ya ci gaba da zama a cikin rundunar, kuma saboda matsayinsa, alƙalin ya ce ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen aikata laifuka.”
Sai dai Eriator ya musanta zarge-zargen, inda ya ce shi ɗan sanda ne kawai, kuma ba ya shiga ayyukan ta’addancin rundunar.
A cewarsa, ya shiga aikin ‘yan sandan Nijeriya bisa raɗin kansa a watan Yunin 2009 kuma ya kai matsayin kofur.
Ya bayyana cewa, an kuma ba shi wuraren binciken ababen hawa a zaɓuka biyu a Nijeriya, ciki har da zaɓen shugaban ƙasa na 2015. An kuma ba shi aiki a rundunar ‘yan sanda ta musamman mai yaƙi da ‘yan fashi da makami (SARS) da aka rusa a Ikeja na wani lokaci kafin ya bar aikin a shekarar 2016.
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya, SARS, ta yi ƙaurin suna wajen take haƙƙin bil’adama da dama kamar karɓar kuɗi, azabtar da waɗanda ake zargi da kai ga munanan raunuka, da kuma kashe-kashe ba busa ƙa’ida ba.
Bayan shafe kwanaki ana zanga-zanga, babban Sufeton ‘yan sanda na lokacin, Adamu Mohammed, ya sanar da rusa rundunar SARS nan take a ranar 11 ga Oktoba, 2020.
A halin da ake ciki dai, shari’ar Eriator ta ƙara yawan jerin sunayen tsofaffin ‘yan sandan Nujeriya da aka hana su zama na dindindin a ƙasar Kanada saboda hannu ko alaƙa da ayyukan ‘yan sanda da ke da alaƙa da aikata laifuka.
A shekarar 2021, mai shari’a Sebastien Grammond ya ƙi amincewa da mafaka ga wani tsohon jami’in SARS, Olushola Popoola, saboda alaƙarsa da ‘yan ta’adda da kuma ‘yan sanda.
Wani tsohon ɗan sanda, Charles Ukoniwe, ya ƙasa samun mafaka a ƙasar Kanada, bayan da alƙalin kotun Patrick Gleeson a Ottawa ya yi watsi da buƙatarsa ta sake duba yadda ya haɗa shi da ƙungiyar ‘yan sandan Nijeriya mai suna MOPOL.
Gleeson ya ce duk ɗan Nijeriya da ya yarda ya shiga aikin ‘yan sandan Nijeriya zai kasance mai laifi ta hanyar haɗin gwiwa a gaban tsarin shari’a na Kanada da kuma yarjejeniyar Majalisar ɗinkin Duniya da ta shafi ‘yan gudun hijira, duk da cewa ba a da tabbacin ya aikata laifukan
