Zaɓen Kamaru: Biya mai shekaru 92 ya ayyana neman tazarce karo na takwas

Spread the love

‘Ya shafe fiye da shekaru 40 a mulki, yanzu kuma yana neman wa’adin mulki na takwas’

Shugaban ƙasar Kamaru, Paul Biya, mai shekaru 92, ya bayyana cewa, zai sake tsayawa takara a zaɓen shugaban ƙasa da za a gudanar a ranar 12 ga Oktoba 2025. Wannan mataki na nufin zai iya ci gaba da zama kan karagar mulki har sai ya kusa cika shekaru 100.

Biya, wanda ya hau mulki tun shekarar 1982, ya bayyana hakan ne ta shafin sa na ɗ (wadda aka fi sani daTwitter), inda ya ce:

“Ni ne ɗan takarar zaɓen shugaban ƙasa na 12 Oktoba 2025. Ku kwantar da hankalinku, domin niyyata na ci gaba da yi muku hidima ya yi dai-dai da manyan ƙalubalen da muke fuskanta. A tare, babu ƙalubalen da ba za mu iya shawo kansa ba. Abin da yafi wannan yana nan tafe.”

Tun kafin wannan sanarwa, Biya ya kasance ɗan takarar jam’iyyar CPDM wadda shi ne shugaban ta. Duk da haka, shekaru da kuma lafiyar shugaban sun zama abin tattaunawa a faɗin ƙasar, musamman ma lokacin da yake ɓacewa daga idon jama’a na dogon lokaci.

A bara, jita-jita game da rasuwar sa sun bazu bayan ya ɓata daga ido fiye da wata guda. Sai dai gwamnati ta ƙaryata wannan jita-jita tare da hana kafofin watsa labarai yin muhawara kan lafiyar sa, tana mai cewa, yana nan da rai kuma yana hutawa a Geneɓa.

A ‘yan watannin baya, wasu daga cikin tsofaffin abokan tafiyar sa sun fara ƙaurace masa. Ministan Kwadago, Issa Tchiroma Bakary, ya yi murabus a watan Yuni domin tsayawa takara a jam’iyyar sa ta FSNC. Haka kuma tsohon Firaminista Bello Bouba Maigari, wanda ya yi kusan shekaru 30 tare da Biya, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar NUDP.

Sai dai ana ganin adawar ba ta da haɗin kai sosai. Maurice Kamto, wanda ya zo na biyu a zaɓen 2018, da kuma Cabral Libii na jam’iyyar CPNR, na cikin waɗanda suka bayyana aniyar su ta tsayawa takara. Ana sa ran za a rufe karɓar takardun tsayawa takara a ranar 21 ga Yuli.

Ko da yake talakawan Kamaru na ci gaba da ƙorafi kan matsalar rashin aikin yi, hauhawar farashi da rashin ingancin ayyukan gwamnati, adawar ƙasar na fama da matsalolin haɗin kai.

Baya ga haka, rikicin ‘yan aware a yankunan da ke magana da Turanci na ci gaba da addabar ƙasar da yawancin al’ummar da ke amfani da Faransanci.

By ukarofi