
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A yau Juma’a ne Shugaba Bola Tinubu zai je Kano domin ziyarar ta’aziyya ga gwamnatin jihar, al’umma da iyalai bisa rashin Hamshaƙin Attajiri marigayi Alhaji Aminu Ɗantata, wanda ya rasu makonni biyu da suak gabata.
Kakakin gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar ranar Alhamis.
Marigayin ya rasu ne bayan shafe shekaru 94 a duniya yana hidimta wa al’umma a gida Nijeriya da wajenta a matsayinsa na ɗaya daga cikin manyan ƴan kasuwa.
Ana sa ran Shugaba Tinubu zai gana da iyalan mamacin tare da miƙa ta’aziyyarsa ta musamman ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da malaman addini a jihar.
A cewar kakakin, Gwamna Abba ya yaba da hoɓɓasan shugaban wajen ƙarfafa haɗin kai da tausayawa musamman a lokacin ake jimamin rashin ɗaya cikin jiga-jigan al’umma.
