Yamal na fuskantar tara kan bikin cikarsa shekaru 18

Spread the love

Gwamnatin Sifaniya ta buƙaci a gudanar da bincike kan cin zarafi da baɗala da ya wuce ƙima da ake zargin an aikata yayin shagalin bikin zagayowar ranar haihuwar fitaccen jarumin ƙungiyar ƙwallon ƙafa na Barcelona, Lamie Yamal.

Gwamnatin ta kuma ce za ta ci tarar ɗan wasan, bayan da ƙungiyar masu kare waada, ta yi zargin an ci zarafin mambobinta bayan da aka gayyaci wasu waadanni tare da wasu ’yan mata 12 masu halitta ta musamman domin nishaɗantar da baƙi a wajen taron bikin cikarsa shekaru 18 da haihuwa.

ɗan wasan na ƙasar Sifaniya ya yi bikin cika shekaru 18 a ranar 13 ga watan Yuli, inda mutane kusan 200 suka halarci bikin, ciki har da abokan wasansa da ’yan uwa da dangi.

A cewar Marca, Yamal zai iya fuskantar tarar da ya kai fam 867,000, kuma babban daraktan masu masu buƙata da musamman a gwamnati, Jesus Martín, ya buƙaci a gudanar da bincike.

By ukarofi