

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Jama’a na yaba wa shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu don yanda ya karrama marigayi tsohon shugaba Buhari da Allah ya yiwa rasuwa bayan fama da jinya a wani asibiti a London.
Musamman masu yabon na cewa shugaba Tinubu ya yi duk abun da ya dace tun daga rasuwar Muhammadu Buhari har zuwa jana’iza a mahaifar sa Daura da ke jihar Katsina.
Duk wasu sun saba da sunan jami’ar Maiduguri wato UNIMAID amma rada ma ta sunan Muhammadu Buhari bai samu wata suka mai yawa ba don yanda hakan ya zama karramawa ga marigayi Buhari wanda ya zama gwamnan soja a jihar arewa maso gabar da ke da helkwatar mulki a Maiduguri.
Wani abun ma da ya kara kayatar da jama’a shi ne jagorantar taron majalisar zartarwa na musamman don karrama marigayin.
Gaskiyar magana marigayi Buhari ya samu karramawar da za a iya cewa ba wani tsohon shugaba da ya samu irin ta a lokacin rasuwar sa watakila sai tsohon shugaba Nnamdi Azikwe.
