
Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta aiyana ranar 10 ha watan Oktoba ta zama ranar yanke hukunci kan bukatar korar kira da shugaban kungiyar IPOB ta ‘yan awaren Biyafara Nnamdi Kanu ya shigar na a kori karar sa don ikirarin ba shi da laifi.
Wannan ya biyo bayan rufe ba da shaida daga masu shigar da kara na gwamnatin Najeriya da gabatar da shaidu 5 da ke alakanta Kanu da cin amanar kasa da ta’addanci.
Babban lauyan gwamnati Adegboyega Awomolo ya ce hakika Kanu ya furta kalaman da su ka tada fitina har a ka kashe jami’an tsaro 170.
Kazalika Awomolo ya kara da cewa da sanin Kanu ya rika ambata cewa shi ne shugaban IPOB da a ka haramta.
Lauyan Kanu Mr.Kanu Agabi ya ce ba wata hujja da a ka bayar da ke tabbatar da Kanu na da alaka da tuhumar da a ke yi ma sa don mutum ne mai cika baki da kuri amma ba ya na nufin tada fitina ba ne.
Bayan kamala sauraron muhawarar manyan lauyoyi sai mai shari’a James Omotosho ya aiyana ranar 10 ga watan Oktoba don yanke hukuncin sake Kanu ko tilasta ma sa ya gabatar da shaidun kare kan sa.
