Shugaban Hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya, Gianni Infantino ya ce sun yi nasarar gudanar da Fifa Club World Cup, kuma sun ɗauki darasa kan yadda za su shirya gasar kofin duniya a Amurka a 2026.
Infantino ya ce FIFA, wadda ta tsara wasannin a Amurka tun daga watan jiya tsakanin ƙungiya 32 ta samu kuɗin da ya kusan kai yuro biliyan 1.5.
Za a rufe labulen gasar ranar Lahadi da karawar ƙarshe tsakanin mai riƙe da Champions League, Paris St Germain da Chelsea mai buga Premier League.
Ana kuma sa ran shugaban Amurka, Donald Trump zai halarcin karawar ƙarshe.
