Tsohon ɗan wasan baya na Manchester United Axel Tuanzebe ya kai ƙarar ƙungiyar bisa zargin ba shi shawarar da ba ta dace ba a kan lafiyarsa.
A makon da ya wuce ne ɗan wasan mai shekara 27, wanda ya koma Burnley daga Ipswich a bazaran nan, ya shigar da ƙara ne a kan United.
ƙarar da danganci wani lokaci ne daga watan Yuli na shekara ta 2022, wanda ya danganci wani rauni da ba a sani ba – wanda kuma ake ganin zai iya cin har sama da fam miliyan 1.
A shekararsa ta ƙarshe a United Tuanzebe, ya tafi jinya tsawon kwana 195, kafin ƙungiyar ta bayar da aronsa ga Stoke a watan Janairun 2023, inda ya yi wasa biyar kawai.
Ya bar Old Trafford a 2023, inda ya koma Ipswich a watan Satumba na wannan shekara inda ya yi wasa 45 har ma ya taimaka wa ƙungioyar ta tsallaka zuwa gasar Premier a 2024.
