Vazquez ya yi bankwana da Real Madrid

Spread the love

Lucas Vazquez ya sanar da yin bankwana da Real Madrid, ba tare da bayyana makomarsa ba.

ɗan wasan wanda ya fara yi wa Madrid wasa tun yana ɗan shekara 16 a 2007 ya sanar da matakin ne a shafinsa na Instagram.

Tun a ranar 13 ga Yuli ne kwangilar shi ta kawo ƙarshe a Madrid.

“A yau bayan buga wasa 400, lokaci ne da zan yi bankwana da ƙungiyar rayuwata. Zan bar Real Madrid amma ba zan taɓa mantawa da Real Madrid ba, inji ɗan wasan mai shekara 34.

Vazquez ya ci awallo 38 a bara, tare taimakawa a ci sau 61, kuma ya lashe kofi 23, da suka ƙunshi kofin Zakarun Turai biyar da kofin La Liga huɗu.

ɗan wasan ya gode wa Real Madrid da kuma magoya bayanta.

By ukarofi