Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya fice daga jam’iyyar PDP ba tare da ɓata lokaci ba.
A wata wasia mai ɗauke da kwanan watan 14 ga watan Yuli, 2025, kuma ya aikewa shugaban jam’iyyar PDP, na gundumar Jada , ƙaramar Hukumar Jada ta jihar Adamawa, Atiku ya bayyana cewa ya fice ne saboda rashin jituwar da ta kunno kai a tsohuwar jam’iyyar mai mulki.
Ya ce ya ga ya zama dole ya fice saboda halin da jam’iyyar ta shiga a halin yanzu, wanda a cewarsa, ya banbanta daga ƙa’idojin da aka kafa jam’iyyar.
Wasiƙar ta ce, “Na rubuta ne domin in yi murabus daga jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) nan take.
“Zan yi amfani da wannan dama domin in nuna matuƙar jin daɗina kan damar da jam’iyyar ta ba ni.
“Yin cikakken wa’adi biyu a matsayin mataimakin shugaban Nijeriya da zama ɗan takarar shugaban ƙasa sau biyu yana ɗaya daga cikin muhimman babi a rayuwata, a matsayina na wanda ya kafa wannan jam’iyya mai kima, haƙiƙa abin takaici ne a gare ni na yanke wannan shawarar.
“Duk da haka, na ga ya zama dole in raba hanya saboda yanayin da jam’iyyar ta shiga a halin yanzu, wanda na yi imanin ya bambanta da ƙa’idojin da muka tsaya a kai, da zuciya ɗaya na yi murabus, na fahimci bambance-bambancen da ba a daidaita su ba.
“Ina yi wa jam’iyyar da shugabanninta fatan alheri a nan gaba. Ina sake gode muku saboda dama da goyon baya.”
An zaɓi Atiku a matsayin mataimakin shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, wanda ya yi aiki a ƙarƙashin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo daga 1999 zuwa 2007.
Ya kuma kasance ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP sau biyu, inda ya daga tutar jam’iyyar a zaɓukan 2019 da 2023. Sai dai Atiku bai yi nasara a zaɓukan biyu na jam’iyyar ba, inda ya sha kaye a hannun Muhammadu Buhari a 2019 da kuma Bola Tinubu a 2023.
Ficewar Atiku daga jam’iyya mai mulki ba zai rasa nasaba da shirye-shiryen zaɓen 2027 ba. Shi da wasu jiga-jigan ‘yan adawa da suka haɗa da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a 2023, Peter Obi, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, sun kafa wata kungiyar hadin gwiwa da nufin tsige Shugaba Tinubu.
A ranar 2 ga watan Yuli ne gamayyar jam’iyyun suka taru domin ɗaukar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a matsayin dandalin kawar da jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) mai mulki a zaɓen 2027 mai zuwa.
Jam’iyyar ADC ta nada tsohon shugaban majalisar dattawa, Daɓid Mark, wanda shi ma ya fice daga jam’iyyar PDP a matsayin shugaban riƙo na ƙasa, inda aka naɗa tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola a matsayin sakataren riƙon ƙwarya na ƙasa.
Wannan dai ba shi ne karon farko da Atiku ya fice daga jam’iyyar PDP domin ci gaba da neman takararsa na shugaban ƙasa a wasu jam’iyyun siyasa ba.
Ya fara ficewa daga jam’iyyar ne bayan ya kammala wa’adinsa na mataimakin shugaban ƙasa a shekarar 2007 a ƙarƙashin jam’iyyar Action Congress of Nigeria (ACN), bayan da jam’iyya mai mulki a lokacin ta fifita tsohon shugaban ƙasa Umar Musa Yar’adua a matsayin tikitin takara.
Atiku ya sha kaye a babban zaɓen ƙasar, inda ya zo na uku bayan Muhammadu Buhari da kuma wanda ya lashe zaɓen, Yar’adua.
Sai dai kuma zai sake komawa jam’iyyar PDP ne domin neman tikitin takarar shugaban ƙasa gabanin zaɓen shugaban ƙasa na 2011 kuma ya sha kaye a hannun Goodluck Jonathan, wanda ya yi nasara a babban zaɓen ƙasar.
Bugu da ƙari, Atiku ya bar jam’iyyar PDP tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar da suka haɗa da Bukola Saraki, Rotimi Amaechi, inda suka koma jam’iyyar gamayyar jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC). Ya rasa tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a hannun Muhammadu Buhari kuma ya ci gaba da mara masa baya domin ya kayar da shugaba Jonathan mai ci.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ci gaba da neman kujerar da ta fi kowa sha’awa a kasar, lamarin da ya sa har yanzu ya sake komawa jam’iyyar PDP a shekarar 2017, inda ya sake lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar, sai dai ya sha kaye a hannun Shugaba Buhari mai ci a zaɓen 2019.
Ya sake daga tutar PDP a zaɓen 2023, inda ya zo na biyu bayan Tinubu. Rikicin da Ministan babban birnin tarayya ya yi na zaɓen fidda gwani na jam’iyyar PDP a 2022 ya haifar da babban rikici a jam’iyyar adawa, wanda ya sa Atiku ya fice daga jam’iyyar a karo na uku.
