Buhari: Fadar Shugaban Ƙasa ta kare jana’izar ƙasa da lissafo nasarorin Tinubu ga ADC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Fadar Shugaban Ƙasa ta kausasa akan jam’iyyar adawa ta ADC bisa kalamanta akan jana’izar ƙasa da aka shirya wa marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, tana mai bayyana hakan a matsayin abinda ake ƙoƙarin siyasanatarwa ko ta wace hanya.

A sanarwar da mai taimaka wa Shugaban Ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare ya fitar, ya zargi ADC da yunƙurin karkatar da tunanin al’umma zuwa siyasa a madadin jimamin ƙasa da ake ciki.

Da fari, ADC ta zargi gwani Shugaba Bola Tinubu da ƙoƙarin siyasanatar da lamarin rasuwar Buhari don cimma wata manufa ta siyasa.

Saidai a yayin martani game da hakan, Dare ya bayyana cewa jam’iyyar tana yin irin kalaman domin ta tozarta kanta a idon al’umma, wanda a cewarsa ba shi ne na farko da ake samun ta a ikirarin irin hakan ba.

Ya ce, jam’iyyar da ke gwagwarmayar neman tantancewa ba ta da hurumin faɗa wa shugaban ƙasa yadda ake mulki ko gudanar da tsare-tsarensa.

Ya kuma ce, an shirya jana’izar ƙasa ne ga marigayin da nufin karrama shi da iyalansa da ɗaukacin al’ummar ƙasa baki ɗaya, wanda ya samu halartar jagororin duniya da miliyoyin ƴan Nijeriya.

Sunday Dare ya kuma lissafo wasu daga cikin nasarorin da gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu ta samu, waɗanda suka haɗa da farfaɗowar darajar naira da daidaito a farashin musayar kuɗaɗen ƙasashen duniya, ƙara adadin samar da mai zuwa ganga miliyan 1.7 a kullum da ƙarin kaso 60 na kuɗaɗen da ake raba wa jihohi daga asusun Tarayya.

Sauran sun haɗa da, gyara harkokin biyan albashi da fansho a jihohi 31, kammala manya ayyana tituna a faɗin ƙasar, samar da tsarin bada lamunin kuɗin karatu ga ɗaliban gaba da sakandare, samar da hukumomin ci-gaban shiyyoyi da suaran su.

By Babaji