Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
An sallami Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, daga asibiti bayan daya kwanta har na kwanaki biyu ƙarƙashin kulawar likitoci sakamakon haɗarin mota da ta rutsa da shi a hanyarsa na komawa Katsina bayan dawowarsa daga Daura.
Mai magana da yawun gwamnan Muhammad kaula ya bayyana haka a wata takardar da ya aike wa manema labarai.
Ya ce likitocin gwamnan sun tabbatar da cewa yana cikin ƙoshin lafiya kuma yana iya komawa bakin aikinshi nan take.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana godiyarsa ga ɗaukacin al’ummar Jihar Katsina, abokai, abokan aiki da duk masu yi mashi addu’a da fatan alheri daga sassa daban-daban na Najeriya.
“Na ji daɗin irin addu’o’i da goyon baya da jama’a suka nuna man. Wannan soyayya ta ƙara mani ƙwarin gwiwa da azama wajen ci gaba da yi ma Jihar Katsina aiki ” in ji Gwamna Raɗɗa.
Gwamnan ya tabbatar da ƙudurin shi na ci gaba da aiwatar da shirin raya ƙasa domin cigaban Jihar Katsina da walwalar al’ummar.
