Shaye-shaye: Wuta ce da ke cin ginin al’umma cikin sirri

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

‘Idan ba ka koya wa yaro bin hanya ba, sai ka biyo shi da kuka a bayan titi.’

Mai karatu barkanmu da sake kasancewa a shafin Iyali. Sannunku da jimirin bibiyar mu. A wannan mako, za mu yi dubiya ne kan ɗabi’a ta shaye-shaye wadda a can da ana mata kallon ɗabi’a ta ‘yan iska, ko waɗanda ba su da mafaɗi.

Saidai a yanzu ta zama ruwan dare, game gari, domin za ka iya samun ta har a wurin ɗalibai masu hazaƙa a ƙoƙarin ganin ba su faɗi jarrabawa ba su afka shaye-shaye da sunan maganin hana su barci. Haka za ka iya samun su a cikin ‘ya’yan malamai, ‘ya’ya mata masu tarbiyya da ma manyan. Matan aure da iyayen mata da yawa sun shiga wannan sahu, kai har ma da manya dattijai.

Matsalar shaye-shaye ba ta tsaya a titi ko ‘yan daba ba, ta shiga makarantu, ta shiga gidajenmu. Akwai yara da ke shan tabar wiwi a bayan makaranta. Akwai ‘ya’ya mata da ke ɗaukar kodin su saka a cikin zobo ko lemo, wanda abin takaici wasu har kallon abin suke a matsayin wayewa.

Me ke janyo shaye-shaye?

Ababe da dama kan iya janyo shaye-shaye, waɗanda wasu da dama kawai zugar shaiɗan ce ke ɗawainiya da su. Yayin da wasu ta dalilin wani abu ne suke faɗawa a ciki, don haka sai dai mu kawo wasu da muke ganin za su iya zama silar shaye-shaye, amma ba dukka ba. Ga su kamar haka;

1. Rashin kulawa daga iyaye.

 2. Abokai marasa tarbiyya.

 3. Sha’awar gwada sabon abu.

 4. Damuwa da matsin rayuwa.

 5. Kallon fina-finai da ke nuna maye a matsayin kwalliya.

 6. Rashin addini ko kula da abinda ya zo da shi.

A wata makaranta a Jihar Niger, an kama yara 8 suna busa ganyen wiwi a bayan ɗakin koyon kimiyya, dukansu suna da shekarun da ba su wuce 14 ba. Wannan kawai ya isa ya tsorata iyaye kan tashi tsaye game da sha’anin shaye-shaye a tsakanin matasa. 

Illolin shaye-shaye ga matasa:

1. Zubar da mutunci da sanya rashin kunya.

2. Rangwanta lafiyar ƙwaƙwara.

3. ƙarancin ilimi.

4. Zama barazana ga iyaye da al’umma.

5. Aikata miyagun laifuka sakamakon gushewar hankali ko imani wanda shaye-shaye kan hadda hakan, kamar fashi da makami, fyaɗe da sauransu.

6. Illata zamantakewar aure ko rushe gida bakiɗaya.

A rahoton NDLEA na shekarar 2024, sama da matasa 1,200,000 a Najeriya suna amfani da nau’in wata kwaya ko giya, yawancin su ‘yan tsakanin shekaru 13 zuwa 27 ne.

Rawar iyaye da al’umma wajen daƙile shaye-shaye:

1. Alaƙa mai kyau da ‘ya’ya: Ka zama abokinsa kafin duniya ta zama abokiyarshi.

2. Sanin abokansa da abubuwan da yake sha’awa.

3. Fadakarwa ba da tsoro ba: A koyar da yara illar shaye-shaye ba tare da tsoro ko tsinuwa ba.

4. Tattaunawa da makaranta da malamai: Don ganin an kafa ƙa’idodi da ladabtarwa.

5. Samun ‘yan sanda da NDLEA su shiga al’umma su wayar da kai.

6. Addini da tarbiyyar gida: Kowane yaro ya taso yana jin karatun ƙur’ani da karantarwa kan haramcin shaye-shaye.

Daga ƙarshe, ya kamata mu sani, shaye-shaye annoba ce da ke ruguza rayuwar matasa a hankali kamar haƙoran kwari. Dole ne iyaye su farka, malamai su shige gaba, iyaye da malamai su haɗa hannu. Ba komai yafi muhimmanci a yau kamar ceto matashi daga halaka.

Kada mu bar wayar salula ko titi su koya wa yaro daidai da kuskure. Mu zama ginshiƙi da garkuwa, domin mu kai ga gobe mai haske, ba rana mai duhu ba. Domin kaso mafi nauyi na ta’addacin da ake a yanzu shaye-shaye ne ke jagorantar su.

By ukarofi