Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars FC ta sanar da naɗin Evans Ogenyi a matsayin sabon mai horarwa ko kuma kocin ƙungiyar, domin jagorantar shirin kakar gasar Firimiya ta Najeriya ta shekarar 2025/2026.
Sanarwar hakan ta fito ne daga shafin sada zumunta na ƙungiyar da yammacin ranar Laraba, inda ta bayyana cewa Evans zai fara aiki nan take ba tare da wani ɓata lokaci ba.
Wannan naɗi ya zama wani komo gida ga Evans Ogenyi wanda ya jagoranci Pillars zuwa samun ɗaukaka zuwa gasar Firimiya (NPFL) a shekara ta 2023, amma daga baya aka sallame shi ba tare da cikakken bayani ba.
Wannan sauyi ya zo ne bayan wani lokaci da ƙungiyar ta fuskanci matsaloli a fagen horarwa da rashin tabbas kan shugabanci. Masana harkar wasanni da magoya baya sun bayyana dawowar Ogenyi a matsayin mataki mai kyau, musamman ganin cewa ya riga ya san ƙungiyar da tsarin ta sosai.
Ƙalubalen da ke gaban sa;
A yanzu haka, sabon mai horarwar zai fuskanci gagarumin aiki na gina ƙungiyar da ƙarfafa ta, domin ba kawai tsayawa a gasar ba, har ma da neman damar lashe kofuna.
Wasu daga cikin manyan ayyukan da ke gabansa sun haɗa da:
Kafa ingantaccen tsari na horarwa da dabarun wasa.
Gina kyakkyawar alaka da ‘yan wasa da shugabancin ƙungiyar
Samun sakamako mai kyau a gida da waje
Kawo sabbin dabaru da horar da matasa masu tasowa
Tun bayan bayyanar labarin, magoya bayan Pillars da dama sun bayyana farin cikinsu da dawowar kocin. Wasu na ganin wannan wata dama ce da Ogenyi zai iya amfani da ita domin tabbatar da ƙwarewarsa, musamman ganin cewa yana da tarihin nasara da ƙungiyar.
Naɗin Evans Ogenyi dai ya nuna cewa Kano Pillars na son dawowa matsayin da take da shi a baya a gasar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya. Idan har aka ba shi goyon baya da kayan aiki, tabbas Pillars na da damar taka rawar gani a kakar wasa mai zuwa.
