Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya samu lambar yabo ta “Gwamnan Shekara ta 2025” daga Jaridar Blueprint, saboda irin gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban ilimi a jihar.
Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya fitar a jiya Talata a Kano, ta bayyana cewa gwamnan ya ware kaso mafi tsoka na kasafin kuɗin jihar zuwa ɓangaren ilimi, wanda ya ɗara sauran jihohi a Najeriya a shekarar 2025.
A wani taro na musamman da aka gudanar don miƙa wannan lambar yabo, Sanusi Dawakin-Tofa, wanda ya wakilci gwamnan, ya ce gwamnatin Abba ta himmatu wajen sauya tafiyar da mulki tare da mayar da hankali kan bunƙasa ilimi da ci gaban rayuwar al’umma.
