
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wata Babbar Kotu a Kano ta yanke wa sanannen ɗan TikTok a jihar, wato AL-Amin G-Fresh hukuncin wata biyar a gidan yari bayan samun sa da laifin wulaƙanta takardun Naira.
Mai Shari’a Sale Musa Shuaibu ya gabatar da hukuncin bayan da Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta maka shi a kotun.
Bayan karanta masa abin da ake tuhumar sa a kai, G-fresh ya amsa laifinsa.
Daga nan ne kotun ta yanke masa hukuncin tare da zaɓin biyan tarar Naira 200,000.
An samu mai laifin ne da watsa bandir-dandir ɗin ƴan dubu-dubu a yayin bikin buɗe shagon wata ƴar TikTok mai suna Rahama Sa’idu a Ƙaramar Hukumar Tarauni dake Jihar Kano a shekarar da ta gabata.
