Majalisar Dattawa ta sahale wa Tinubu ya ciyo bashin dala biliyan 21

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

A ranar Talata, Majalisar Dattawa ta amince da shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na neman bashin waje sama da dala biliyan 21 domin gudanar da kasafin kuɗin shekarar 2025–2026, wanda hakan zai bai wa gwamnati damar aiwatar da dokar kasafin kuɗin 2025 gaba ɗaya.

Shirin bashin da aka amince da shi ya haɗa da dala biliyan 21.19 ($21.19bn) na rancen waje kaitsaye, Euro biliyan 4, Yen biliyan 15, kyautar tallafi ta dala miliyan 65, da kuma rancen cikin gida ta hanyar takardun bashi na gwamnati da jimillar su ta kai kusan Naira biliyan 757.

Haka kuma an tanadi damar tara har zuwa dala biliyan 2 ta hanyar amfani da kayan aikin kuɗi da aka bayyana da kuɗin waje a kasuwar cikin gida.

Amincewar ta biyo bayan gabatar da rahoto daga Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Bashin Cikin Gida da na Waje, Sanata Aliyu Wamakko, wanda ya bayyana cewa an fara miƙawa Majalisar shirin bashin a ranar 27 ga Mayu, amma aka samu jinkiri saboda hutun majalisa da wasu matsalolin takardu daga Ofishin Gudanar da Basussuka na ƙasa (DMO).

Shugaban Kwamitin Kasafin Kuɗi na Majalisar Dattawa, Sanata Olamilekan Adeola, ya bayyana cewa yawancin buƙatun bashin tuni an riga an haɗa su cikin Tsarin Kudin Shiga na Tsakanin Lokuta (MTF) da kuma kasafin kuɗin shekarar 2025.

By ukarofi