Hare-haren ‘yan bindiga: Gwamnan Kaduna ya ƙaddamar da gidaje ga waɗanda suka rasa matsuguni

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, a ranar Talata ya ƙaddamar da zagaye na farko na gidajen ƙatar Sanabil Project, wanda ya haɗa da gidaje, makaranta, asibiti da kasuwa, domin tallafawa waɗanda suka rasa matsuguni sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a sassan jihar.

Shirin, wanda aka aiwatar tare da haɗin gwiwar gidauniyar ƙatar Charity, zai samar wa waɗanda hare-haren ‘yan bindiga ya sa suka rasa matsuguninsu a jihar da aka yi ta fama da fiye da shekaru 10 da suka wuce.

Yayin jawabi a wajen bikin ƙaddamarwar da aka gudanar a Kaduna, Gwamna Sani ya bayyana lamarin a matsayin “ɗaya daga cikin mafi muhimmanci a rayuwarsa.

“Ina tsaye a tsakanin waɗannan sababbin gidaje, tare da iyalan da suka jure wa rashin da ba a misaltuwa ba, ina furta da tabbaci cewa wannan shi ne mafi muhimmanci a rayuwata ba a matsayin Sanata ko Gwamna ba, amma a matsayina na ɗan Adam.”

Gwamnan ya bayyana cewa shirin ba wai gina gine-gine kawai ba ne, amma “aiki ne na warkar da raunuka, cika alƙawari, da tabbatar da amana.

“Wannan sakonmu ne ga kowace mace, maraya, da wanda aka raba da gidansa: ba a manta da ku ba. Muna tare da ku, muna girmama ku.”

Har ila yau, ya bayyana cewa an raba kayan tallafi da suka haɗa da babura masu ɗaukan kaya, injinan niƙa, kayan gyaran gashi, da injinan walda domin taimakawa waɗanda bala’in ya shafa su koma kasuwanci da sana’o’insu.

“Mun fahimci cewa gyaran rayuwa na dindindin na buƙatar hanyoyin samun dogaro da kai,” inji Gwamnan.

Mai ba Shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, wanda ya wakilci Shugaba Bola Tinubu a wajen bikin, ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya na ƙoƙarin tabbatar da dawowar doka da oda a faɗin ƙasarnan.

“Nijeriya na hannun waɗanda suka damu da ita kuma za su iya rike ta su kareta daga dukkan matsaloli. Za mu dawo da doka da oda, wannan shi ne tabbacin da muke bayarwa,” in ji Ribadu.

Shugaba Tinubu ya yabawa tsarin zaman lafiya na gwamnatin Una Sani, wata ‘Peace Model’ wanda ya dogara da hadin kai da fahimta tsakanin al’umma, yana mai cewa komawar manoma da buɗe kasuwar Birnin Gwari alama ce ta dawowar zaman lafiya a faɗin jihar.

“Muna share hawayen waɗanda rikici ya shafa. Muna basu gurbin kasancewa cikin al’umma,” daga nan sai ya mika godiya ga gidauniyar ƙatar Charity bisa wannan ɗawainiya da ya yi.

Tinubu ya jaddada cewa yaƙi da ta’addanci na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta fi bai wa muhimmanci.

By ukarofi