Daga RABIU SANUSI a Kano
Hukumar Kula da Zirga-Zirgar Ababen Hawa ta Jihar Kano (KAROTA), ta gudanar da taron wayar da kai na musamman akan illolin shan miyagun ƙwayoyi, tare da haɗin gwiwar hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA).
Taron, wanda aka gudanar a babban ofishin KAROTA da ke titin Club Road, ya sami halartar wakilan NDLEA da suka gabatar da kwararrun bayanai akan barazanar da miyagun ƙwayoyi ke yi ga tsaron hanyoyi da lafiyar al’umma.
An mayar da hankali kan tasirin shaye-shaye wajen haddasa hatsarori, rashin da’a da rikicewar zamantakewa musamman tsakanin direbobi da matasa masu mu’amala da tituna.
Shugaban hukumar KAROTA, Engr. Faisal Mahmud Kabir, wanda ya jagoranci taron, ya bayyana cewa wannan mataki na daga cikin sabbin shirye-shiryen hukumar wajen karfafa tsaro, inganta tarbiyya da kare rayuka da dukiyoyi a tituna.
“Mun fahimci cewa daya daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa barazana ga hanyoyinmu shi ne shaye-shaye. Wannan taro ba zai tsaya a nan ba. Muna da shirin zurfafa wayar da kai a cikin gida da waje,” inji Engr. Faisal.
A cikin jawabin nasa, Engr. Faisal ya sha alwashin shirya babban horo na mako guda ga ɗaukacin ma’aikatan KAROTA, wanda NDLEA za ta jagoranta. Taron horon zai kunshi ilimin gane masu shaye-shaye, dabarun yaki da safarar kwayoyi, da hanyoyin kare kai daga kamuwa da halayen masu amfani da su.
Baya ga haka, shugaban hukumar ya bayyana ƙudirin KAROTA na ƙarfafa haɗin gwiwa kai-tsaye da NDLEA a matsayin abokan aiki kafaɗa da kafaɗa, domin tabbatar da tsaro, da kariya daga miyagun dabi’u a tsakanin al’umma da masu sana’ar sufuri.
A nasa ɓangaren, wakilan NDLEA sun yaba da matakin da KAROTA ta dauka, suna mai cewa wannan haɗin kai na da matukar muhimmanci wajen samar da ingantaccen tsaro da lafiya a faɗin Jihar Kano.
