Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar kiyaye haɗurra ta Jihar Katsina (KASSAROTA)ta ƙirƙiro sashen kula da ƙorafe-ƙorafen al’umma. Sashen wanda yake ƙarƙashin ofishin jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, zai yi aiki don karɓar ƙorafe-ƙorafen al’umma da suka shafi yadda jami’an hukumar suke gudanar da ayyukansu.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar Abubakar Marwana ya sanar da haka a wata takarda ɗauke da sa hannun sa wanda aka rabawa manema labarai a Katsina.
Ya bayyana cewa ƙorafe ƙorafe akan matsalolin cin hanci da rashawa, amfani da ƙarfi ko matakan da basu dace ba na tursasawa al’umma, ko rashin bin ƙa’idojin aiki a yayin gudanar da ayyukansu”duk wannan sashi zai saurara.
Sashen kuma ya ce zai karɓi shawarwarin al’umma akan yadda za a inganta ayyukan hukumar don tsare lafiya da dukiyoyin al’ummar Jihar Katsina.
A cewar Marwana wannan mataki na daga cikin sabbin matakan da gwamnatin Dikko Raɗɗa take ɗauka don inganta ayyukan hukumar, kare mutuncin al’ummar Jihar, tsare rayuka, lafiya da dukiyoyin al’umma.
Haka kuma kafa sashen na da nufin rage yawan ƙorafe ƙorafen al’umma akan cin zarafi, cin hanci da rashawa, ko sanya karfi da ya wuce ƙa’ida a yayin gudanar da ayyukan jami’an, acewar jami’in hulɗa da jama’a na hukumar.
“Harwala yau sashen zai riƙa gudanar da bincike don tabbatar da sahihancin ƙorafe-ƙorafen da aka kawo kafin ɗaukar matakin da ya dace akan jami’an.
Sai dai, hukumar tayi kira ga al’ummar Jihar Katsina musamman masu amfani da ababen hawa, da su kiyaye dokokin da aka gindaya don kare lafiyarsu da dukiyoyin su ya ce.
Ya bayyana hukumar KASSAROTA a matsayin hukuma ce da aka ƙirƙiro don tsare rayuka da dukiyoyin al’umma daga haɗurran a lokuttan gudanar da harkokinsu na yau da kulluma. Ba hukuma bace ta cin zarafi, tilastawa ko tsanantawa wani ko wasu al’umma ba.
“Hukumar ta alƙawarin kare mutunci da yancin al’ummar Jihar Katsina a lokuttan gudanar da ayyukan jami’an ta,”Marwana ya ce.
Daga nan sai hukumar ta shawarci masu ababen hawa da su cika dukkan ƙa’idojin da hukumar ta kayyade, tare da kiyaye dokokin hanya a matsayin babbar hanya ta kaucewa hukuncin da doka ta tanada.
