Shugaban ƙasar Gambiya Adama Barow ya kawo ziyarar ta’aziyar Buhari Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Shugaban ƙasar Gambiya Adama Barrow tare da Uwargidansa sun kawo ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi tsohon Shugaban Ƙasa marigayi Muhammadu Buhari a gidansa dake garin Daura

Barow ya bayyana rasuwar Muhammadu Buhari a matsayin babban rashi bama a ƙasashen Afrika ba harma da duniya baki ɗaya.

“Duniya tayi rashin shugaba adali mai son zaman lafiya da daidai a tsakanin ƙasashen Afrika da sauran manyan ƙasashen duniya masu ƙarfin tattalin arziki,”inji Adama Barow.

Ya ce ƙasar Najeriya da ƙasashen Afirka zasu rinka tunawa da marigayi Muhammadu Buhari bisa aƙidar ta tabbatar da gaskiya da riƙon amana da kuma yaƙi da rashin ɗa’a wanda yace da yawa ƙasashen Afrika sunyi koyi da shi.

Shugaban ƙasar Gambiya yayi addu’ar Allah masa rahama.

Daga baya shugaban ƙasa Adama Barow ya sanya hannu a littafin rajista.

A jawabin sa Yusuf Buhari babban ɗa ga marigayi Muhammadu Buhari a madadin iyalan marigayin ya nuna jin daɗin sa da wannan ziyara da shugaban ƙasar tare da uwargidansa suka kawo masa ,yayi fatan Allah maida su ƙasar su lafiya.

By ukarofi