Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Gwamnatocin Tarayya, Jihohi da ƙananan Hukumomi sun raba jimillar Naira Tiriliyan 1.818, na kuɗaɗen shiga daga asusun tarayya a watan Yunin 2025.
Sanarwa da Kwamitin Rabon Kuɗaɗen Asusun Tarayya (FAAC) ya fitar ranar Asabar a Abuja, bayan taron kwamitin ya bayyana cewa, kuɗaɗen shigar da ake rabawa na Naira Tiriliyan 1.818 sun haɗa da kuɗaɗen shiga da aka ƙayyade na doka na Naira Tiriliyan 1.018, kuɗaɗen shiga na haraji ɓAT na biliyan N631.507.
A cewar FAAC, jimillar kuɗaɗen shiga na Naira Tiriliyan 4.232 ya kasance a cikin watan Yunin 2025. Jimillar kuɗaɗen da aka cire na kuɗaɗen da aka samu ya kai Naira biliyan 162.786.
Sanarwar ta ci gaba da bayyana cewa, an samu jimillar kuɗaɗen shiga na Naira tiriliyan 3.485 na watan Yunin 2025. Wannan ya ce, ya haura Naira Tiriliyan 2.094 da aka samu a watan Mayun 2025 da Naira Tiriliyan 1.390.
Jimillar kuɗaɗen da aka samu na Naira biliyan 678.165 da aka samu daga harajin ɓAT a watan Yunin 2025, ya yi ƙasa da Naira biliyan 742.820 da ake samu a watan Mayun 2025 da Naira biliyan 64.655.
Sanarwar ta bayyana cewa, daga jimillar kuɗaɗen shigar da ake rabawa na Naira Tiriliyan 1.818, Gwamnatin Tarayya ta samu jimillar Naira Biliyan 645.383, sannan gwamnatocin Jihohin ƙasar sun samu jimillar Naira Biliyan 607.417.
Majalisar ƙananan Hukumomi ta samu Naira Biliyan 444.853, yayin da aka raba Naira Biliyan 120.759 (kashi 13 na kuɗaɗen shiga na ma’adinai) ga jihar da ta samar da kuɗaɗen shigar.
A kan kuɗaɗen shiga na Naira Tiriliyan 1.018 da aka raba bisa ƙa’ida, sanarwar ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta samu Naira Biliyan 474.455, sannan gwamnatocin jihohi sun karɓi Naira Biliyan 240.650.
ƙananan Hukumomin sun samu Naira Biliyan 185.531 sannan an raba Naira Biliyan 118.256 (kashi 13 na kuɗaɗen shiga na ma’adinai) ga jihohin da suka fi samar da kuɗaɗen shigan.
