Gwamnatin Tarayya ta gargaɗi al’umma kan yaɗuwar wasu manyan cututtuka

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Darakta Janar na Cibiyar Kula da Cututtuka ta Nijeriya (NCDC), Dokta Jide Idris, ya yi gargaɗin cewa an gano ɓullar cututtuka kamar zazzaɓin dengue, shawara, kwalara, mashaƙo da kuma Mpox zai haifar da mummunar illa ga al’ummar Nijeriya fiye da yadda aka saba gani a baya.

Da yake magana a gidan Talabijin na Channels a shirin The Morning Brief a ranar Litinin, Dokta Idris ya bayyana damuwar cewa yawancin masu fama da zazzaɓin Dengue ana kuskuren sa da zazzaɓin cizon sauro, wanda ke haifar da tsaiko wajen magance cutar da kuma rashin ɗaukar matakan da suka dace.

“Abin takaici, zazzaɓin dengue yana da alamomi da yawa daban da zazzaɓin cizon sauro, domin shi zazzaɓinsa ya fi tsanani, inda ya haɗa da ciwon kai da kasala, wanda ke kai mutane da samun magani na daban,” inji Idris.

Ya yi gargaɗin cewa rashin kai rahoton waɗannan cututtuka ga hukumomin kiwon lafiya na yin illa ga tsaron lafiyar ƙasa da kuma kawo cikas ga ƙoƙarin mayar da martani kan lokaci.

“Abun da ya kamata a fahimta shi ne, idan mutane ba su kai rahoton kamuwa da cutar ba, ta na ci gaba da yaɗuwa ne a tsakanin al’umma.

Adadin ƙararrakin da muka samu, adadin ƙarfin da za a ƙara sakawa,” inji shi.

Dakta Idris ya bayyana cewa, a lokuta da dama ba a iya maganin cutar zazzaɓin Dengue, wanda hakan ya sa cutar ta ƙara yaɗuwa kafin a sanar da hukumomin lafiya.

“A kan shafe har tsawon makonni biyu ko uku kafin a sanar da mu,” inji shi.

Ya jaddada matuƙar buƙatar ƙwararru a fannin kiwon lafiya, musamman waɗanda ke manyan makarantun gaba da sakandare, su riƙa kai rahoton ɓullar cutar da aka tabbatar ko kuma waɗanda ake zargi cikin gaggawa ta hanyar ma’aikatun lafiya na jiha ga NCDC.

“Da zarar an gano wani lamari a kowane wuri, musamman a asibitocin koyarwa ko na jami’o’in da ke da ƙarfin gano cutar, ya kamata a ba da rahoton nan da nan don ba da damar mayar da martani da wuri.”

Idris ya kuma shawarci ‘yan Nijeriya da su guji shan magani da kansu, maimakon haka su nemi kulawar da ta dace a lokacin da suka gamu da alamu kamar zazzaɓi mai zafi, kasala, da kuma ciwon gaɓoɓi.

“Muna ba da shawara koyaushe mutane kada su ɗauka cewa kowane zazzaɓi cizon sauro ne, dole ne ku ziyarci wurin kiwon lafiya inda za a iya gano ainihin cutar,” inji shi.

Tun da farko dai NCDC ta fitar da sanarwar kiwon lafiya ga al’umma a faɗin ƙasar a ranar 18 ga Yuli, 2025, biyo bayan ɓarkewar cutar kwalara, zazzaɓin dengue, mashaƙo, da kuma Mpoɗ a yankuna daban-daban.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a shafinta na yanar gizo, ta bayyana lamarin a matsayin “babban abin da ya shafi lafiyar jama’a” da ke buƙatar kulawar ƙasar nan da nan da kuma ɗaukar matakan da suka dace.

“Halin da ake ciki yana buƙatar a sanya ido sosai tare da tsaurara matakan mayar da martani daga dukkan masu ruwa da tsaki,” inji NCDC.

Hukumar ta yi gargaɗin cewa idan ba a ɗauki matakan gaggawa a kowane mataki ba tun daga ma’aikatan kiwon lafiya na gida zuwa masu tsara manufofin tarayya, ɓarkewar cutar na iya shiga cikin gaggawa na kiwon lafiya.

Dokta Idris ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su ba hukumomin lafiya haɗin kai, da bayar da rahoton ɓullar cutar da ba a saba gani ba, tare da bin shawarwarin hukuma don hana ci gaba da ɓarkewar wannan annoba.

“Wannan faɗakarwar ba don haifar da firgita ba ce, amma don wayar da kan jama’a. Dole ne mu sanar da mutane haɗarin da muke fuskanta da abin da za mu yi. Ba da rahoto da wuri zai iya ceton rayuka da kuma iyakance yaduwar cututtuka,” inji shi.

Hukumar ta NCDC ta kuma kunna hanyoyin ba da agajin gaggawa kuma tana aiki tare da gwamnatocin jihohi, asibitoci, da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa don daƙile ɓarkewar cutar tare da inganta wayar da kan jama’a.

Yayin da Nijeriya ke fama da barazanar kamuwa da cututtuka da dama, hukumomin lafiya na kira ga ’yan ƙasar da su kasance cikin shiri, su nemi magani da wuri, da kuma bijirewa neman magani da ka ba tare da tuntuɓar ƙwararru ba.

By ukarofi