Fadar Shugaban ƙasa ta caccaki ADC kan sukar sigar jana’izar Buhari

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Fadar Shugaban Nijeriya ta mayar da martani kan zargin da jam’iyyar haɗaka ta ADC ta yi na cewa, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na amfani da rasuwar tsohon shugaba Muhammadu Buhari, don samun tagomashi na siyasa da neman karɓuwa a idon jama’a.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare ya bayyana zargin na ADC a matsayin “abin kunya,” inda ya ce jam’iyyar ce ke amfani da rasuwar Buhari don neman suna.

ADC dai ta ce gwamnatin Tinubu ta yi amfani da yadda aka gudanar da jana’izar Buhari da kuma yadda aka shirya bikin bankwana da shi a Daura da ke jihar Katsina, domin ƙara samun karɓuwa a idon ’yan ƙasa. 

Fadar shugaban ƙasar ta ce marigayi Muhammadu Buhari ya cancanci yi masa jana’izar ban-girma kuma sun yi haka ne don girmamawa saboda hakan ne ya dace da shi a matsayinsa na tsohon shugaban ƙasa.

ɓangarori da dama a Nijeriya sun yaba da karramawar da gwamnatin ta Tinubu ta yi wa marigayin, sai dai masu suka sun ce gwamnatin na yi ne domin “lallaɓa masoya tsohon shugaban ƙasar da nufin janyo su a jiki”.

A yayin da take kare yadda gwamnatin Tinubu ta gudanar da jana’izar Buhari, fadar shugaban ƙasar ta jaddada cewa an gudanar da shi cikin cikakkiyar girmamawa, wanda ya dace da gadon tsohon jagoran, kuma ‘yan Nijeriya sun sa ido sosai kuma shugabannin ƙasashen duniya sun amince da shi.

Sanarwar ta kuma sake fitar da abin da ta kira nasarorin da gwamnatin ta samu, waɗanda suka haɗa da daidaita Naira, ƙara yawan man fetur, inganta rabon kuɗaɗen FAAC, ci gaban ababen more rayuwa, da aiwatar da asusun ba da lamuni na ilimi na Nijeriya (NELFUND) da tsarin basussuka.

Ana kallon Buhari a matsayin ɗaya daga cikin ’yan siyasa mafiya karɓuwa tsakanin al’umma a tarihin Nijeriya.

ADC, jam’iyya ce wadda ’yan siyasa masu adawa da gwamnatin ƙasar suka tare a cikinta da nufin haɗa ƙarfi wajen yaƙar jam’iyyar APC mai mulki a babban zaɓen ƙasar da za a yi a 2025.

By ukarofi