Daga MUHAMMADU MUJITABA KANO
Malam Idris Daneji Babban Daraktan Makarantar Tropical College Of Health Science And Technology ya bayyana cewa dalilin tsayawar mu tsayin daka na ganin sai mun koyar da ilimin kula da lafiya da kuma cikakkiyar tarbiyya a makarantar koyon kula da kiwon lafiya ta Kwalejin Tropical da ke Kano ya sa har ɗalibai ke kiran makarantar da gidan gyaran hali, inda wannan yana faranta mana rai kuma yana bamu ƙwarin gwiwa na cewa ɗalibin da ba zai yadda ya samu kyakkyawar tarbiyya to ba shakka da kan shi zai kori kansa mu huta da shi ya huta da mu wanda babban burinmu ilimi da bada kyakkyawar tarbiyya ta yadda ɗalibi in ya je aiki zai tausasawa al’umma musamman marasa lafiya da masu jinya ta hanyar yin kyakkyarwa mu’amala da ta dace da kowa da kowa a rayuwa.
Daneji ya bayyana hakan ne a lokacin bikin ratsar da ɗalibai 81 da suka kammala makarantar a wannan lokaci.
Haka kuma ya ƙara da cewa ɗalibai guda 81da aka rantsar daga matakin masu ratsarwa na ƙasa guda 10 daga cikin su akwai CHEW sai kuma JCHEW guda 10 waɗanda suka samu satifiket sai kuma masu yawan da suka yi diploma a wannan fani domin dai samar da kwararru wajen aikin kula da lafiyar alumma inda kuma y ace wannan kwalejin za ta cigaba da yin wannan tsari na tabbatar da tarbiyyar ɗalibai a Tropical College da ke Kano.
