
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A wani yunƙuri na kare haƙƙin karɓar kuɗaɗen amfani na Ƙungiyar masu fina-finai da waƙoƙi ta Ƙasa (AVRS), Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta jaddada cigaba da aiki da ƴancin ƙungiyar ga otal da wasu wuraren kasuwanci.
Mai Shari’a, Obiora Egwuatu, wanda ya gabatar da hukuncin, ya yi watsi da ƙara aka AVRS, wadda otal ɗin Reiz Continental ya shigar inda ya nemi kotun ta yi hukuncin kada a tilasta masa biyan kuɗin amfani da fina-finai daga tashoshin dish.
A hukuncin da Alƙalin ya yi, ya ce wajibi a biya mambobin AVRS haƙƙoƙinsu duab da yadda dokar ƙasa ta tanada.
Akan haka ne kotun ta yi watsi da buƙatar ota ɗin kasancewar rajista da tashoshin da ke haska fina-finai ko waƙoƙin sh ike wajabta biya ga dukkan wanda ya yi.
Haka kuma, kotun ta ce tunda otal yana amfani da kayayyakin sadarwa da ya shafi AVRS wajen kasuwanci ba tare da sahalewar ƙungiyar ba, lamarin da a cewarta saɓa wa doka ne.
Da yq ke magana bayan shari’ar, lauyan mai kare ɓangaren AVRS ya ce hukuncin ba nasara ce ga ƙungiyar da mambobinta da ma harkar shari’ar baki ɗaya.
