
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jami’an rundunar sojoji da ke ƙarƙashin Atisayen FANSAN YAMMA, sun yi nasarar halaka shahararren jagoran ƴan bindiga, Ɗan Ɗari Biyar yayin wani atisaye a yankin yammacin Ƙaramar Hukumar Sabon Birni dake Jihar Sakkwato.
Wata majiya mai ƙarfi a Hedikwatar Sojoji ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai (NAN) cewa lamarin ya auku ne a ranar Alhamis.
Ta ce, ɗan ta’addan ya haɗu da ajalinsa ne a lokacin da ya ke yunƙurin karɓar kuɗin fansa a hannun ƴan uwan waɗanda ya yi garkuwa da su a wani daji da ke tsakanin ƙauyukan Turtsawa, Mazau da kuma Zango.
Majiyar ta kuma ce, ɗan bindigan ya shahara wajen yin kisan gilla ga waɗanda ya yi garkuwa da su da wulaƙanta su kafin neman a biya maƙudan kuɗaɗen fansa akan su.
Ta ƙara da cewa, atisayen wani ɓangare ne na ƙoƙarin shafe ƴan bindiga da maɓoyarsu a jihar da ma shiyyar Arewa maso Yamma baki ɗaya.
An gudanar da atisayen ne a ƙarƙashin shirin bada kariya ga ƙauyuka da gwamnatin jihar ta samar wanda sojoji da ƴan sa-kai suka ƙaddamar.
Haka kuma an yi nasarar ƙwato wasu muggan makamai yayin farauto ƴan bindigar da suka tsere.
