
Dafa BELLO A. BABAJI a Abuja
Kwamishinan Sufuri na Jihar Kano, Alhaji Ibrahim Namadi ya janye a matsayin wanda ya yi lamuni a shari’ar da ake yi tsakanin Gwamnatin Tarayya da Sulaiman Aminu Ɗanwawu a Babbar Kotun Kano.
A wata takarda da aka kai wa mataimakin rajistiran kotun, Namadi ya bada waɗansu dalilai na kansa da suka saka shi ɗaukar matakin, yana mai cewa yana da muhimmci ya kare mutuncinsa da na ofishinsa a matsayinsa na ma’aikacin gwamnati.
Ya ce, ya ɗauki matakin tsaya wa wanda aka gurfanar ne duba da cewa doka ta bada damar haka da danganta ta jini da ke tsakaninsu da kuma tausayi irirn na ɗan-adam.
Ya kuma ce, bai dace a fassara matakin da sunan yana ƙoƙarin taimaka wa ci-gaban ayyukan ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ba.
Sannan, ya jaddada cigaba da yin biyayya ga Gwamna Abbas Kabir Yusuf na jihar Kano da majalisar manyan jami’an gwamnatin jihar gami da ɗaukacin al’ummar jihar, yana mai cewa zai cigaba da bada goyon baya ga ƙoƙarin gwamnatin waje daƙile ayyukan ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a jihar.
A ƙarshe, ya ce zai bada ƙarin bayani akan lamarin yayin da aka buƙaci hakan daga gare shi don tabbatar da gaskiya da adalci.
