Dikko Raɗɗa ya taya Barista Murtala Aliyu murnar samun muƙamin lauyan APC na ƙasa

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Wannan na ƙunshe ne a wata takardar sanar da babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar Muhammad kaula ya sanya wa hannu ya kuma aike wa manema labarai.

Gwamnan ya bayyana wannan nasarar a matsayin abin alfahari da kuma shaida ta yadda jam’iyyar ke girmama ƙwarewa, gaskiya da ingantaccen shugabanci a fannin shari’a.

A cewarsa, wannan naɗin ya zo a kan gaɓa, musamman a daidai lokacin da jam’iyyar ke ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kai da gina dimokuraɗiyya mai inganci a cikin gida.

Ya ce Barista Kankia mutum ne da ya shafe shekaru a fagen hidimar jama’a da aikin lauya, kuma jam’iyyar APC za ta ci gajiyar ƙwarewarsa da halayensa na ƙaunar gaskiya.

“Barista Murtala Kankia shahararren lauya kuma ƙwararre da yake tsayin daka ga jam’iyya,ga hangen nesa da kuma natsuwa a lokutan matsin lamba. Naɗinsa ya dace da lokacin da ake ciki,” in ji Gwamna Raɗɗa.

Gwamnan ya kuma tunatar da irin gudunmuwar da Kankia ya bayar a baya lokacin da ya riƙe mukamin Kwamishinan tarayya da kuma muƙaddashin shugaban hukumar ladabtar da ma’aikata (Code of Conduct Bureau), yana mai cewa hakan ya nuna ƙwazonsa da hazaƙarsa a fagen shugabanci.

Gwamna Raɗɗa ya bayyana tabbacin cewa ƙarƙashin jagorancin Barista Kankia, ayyukan lauya na jam’iyyar APC za su kasance bisa gaskiya, bin doka da kare ƙimar kundin tsarin mulki.

Gwamna Raɗɗa ya shawarci sabon Lauyan jam’iyyar wanda ɗan asalin ƙaramar hukumar kankia ne da ya mai da hankali wajen tabbatar da adalci, haɗin kai da mutunta dokoki a cikin jam’iyya.

“A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Katsina, muna taya Barista Murtala Aliyu Kankia murna bisa wannan sabon aiki da aka ɗora masa a matakin ƙasa. Muna roƙon Allah ya ba shi ikon sauke nauyin da ke kansa cikin nasara.

By ukarofi