Kotu ta tasa ƙeyar ɗan TikTok zuwa gidan yari bayan yaɗa jita-jitar rasuwar Tinubu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wata Babbar Kotun Shari’a a Abuja ta tura wani ɗan Soshiyal Mediya mai suna Ghali Isma’il zuwa gidan yari dake Keffi bayan da wani bidiyon da ya yaɗa kan ƙaryar rasuwar Shugaba Bola Tinubu ya karaɗe kafafen sadarwa.

Jami’an ƴan sandan farin kaya, DSS ne suka kama shi kwanaki kaɗan da ɗora bidiyon a manhajar TikTok, inda ya yi zargin cewa Tinubu ya rasu bayan fama wani rashin lafiya mai tsanani.

Kotun ta yanke wa matashin mai shekaru 29 ɗan yankin Jogana a Ƙaramar Hukumar Gezawa ta jihar Kano hukuncin ne bayan samun sa da laifin yaɗa bidiyon ƙarya da ke nuna cewa ya samun labarin rasuwar shugaban ta majiya mai ƙarfi, wanda ya shiga mawuyacin hali bayan sanya masa guba a abinci, lamarin da ya haddasa ruɗani acikin al’umma.

Akan haka kotu ne ta ce ya saɓa wa dokar ƙasa sashe na 418 a kundin 2004.

Bayan sauraron lauyoyin da ke kare wanda ake tuhuma da na waɗanda suka shigar da ƙara, Alƙalin ya yanke hukuncin tsare Isma’il a gidan gyaran hali na Keffi, jihar Nasarawa.

Daga nan sai aka ɗage shari’ar zuwa ranar 19 ga watan Agusta, 2025.

By Babaji